NATO za ta kara harzuka Rasha kan bukatar Finland da Sweden

Ministocin harkokin wajen kungiyar tsaro ta NATO za su gana a Berlin, babban birnin kasar Jamus nan gaba yayin da Sweden da Finland ke dab da shiga kungiyar kawancen ta kasashen Yamma.

Bayan kwashe shekaru suna zaman 'yan-ba-ruwanmu, kasashen biyu sun ga gagarumin sauyi a ra'ayin jama'arsu na bukatar shiga kungiyar, sakamakon mamayen da Rasha ta yi wa Ukraine.

Tun a ranar Juma'a Rasha ta katse wutar lantarkin da take sayar wa Finland, bisa zargin kin biyanta kudin wutar da ta bayar na baya.

Tsawon shekara da shekaru kasashen na Finland da Sweden sun kasance kawaye kungiyar NATO na kurkusa, amma kum b tare da sun kasance mambobinta ba.

Mambobin kungiyar ba za su saurara ba muddin Rasha ta sake ta kai wa daya daga cikinsu hari, za su mayar da martani kasancewar hakan zai zama tamkar hari ne a kan dukkanin kasashen kungiyar ta NATO, gaba daya.

A kwanakin da ke tafe ne dai 'yan kasashen na Finland da Sweden za su yanke shawara ta karshe kan batun shigar kasashen cikin kungiyar kawancen.

Idan har suka shiga, to ke nan zai kasance Rasha za ta fuskanci mambobin NATO tun daga yankin tekun Arctic har zuwa, bahar Aswad, wato bakin teku.

Daman kuma fadan da gwamnatin Rasha ke yi shi ne, cewa kara girma ko fadadar NATO, wata tsokana da karin barazana ce ga tsaronta - abin da ta lashi takobin mayar da martni a kai.

Dole ne sai dukkanin kasashen kungiyar tsaron ta NATO 30, sun amince da bukatar shigar ta Finland da Sweden da murya daya, kafin ta samu karbuwa.

Zuwa yanzu dai Turkiyya ce kadai take magana a kan kin amincewa da wanan mataki na karbar kasahen biyu a kungiyar, bisa dalilin cewa dukkanin kasashen biyu sun kasance mafaka ga kungiyoyin 'yan ta'adda, abin da ake ganin gwamnatin Turkiyar na nufin kungiyoyin masu fafutuka da makamai na Kurdawa.