Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An fara kai ruwa rana a APC gabanin zaben yan takarar gwamna
A ranar Alhamis ne ake sa ran jam`iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta gudanar da zaben fid da gwani a tsakanin masu neman takarar mukamin gwamna a fadin kasar.
Sai dai yayin da ake tsammanin zaben zai kasance da sauki a wasu jihohin, a wasu kuwa alamu na nuna cewa da wahala ba a kai ruwa rana ba.
Daya daga cikinsu akwai jihar Sakkwato, inda wasu 'ya'yan jam'iyyar ke zargin ana kokarin yi musu babakere, har ta kai ga ana yunkurin hana su ganawa da deliget-deliget.
A hira da BBC Isah Jabbi Usman, wanda shi ne Shugaban magoya bayan jam'iyyar a jihar ta Sokoto, ya ce abin da ke faruwa a jihar bai yi kama da dimukradiyya ba.
Ya ce sun samu labarin yadda ake killace deliget-deliget ana cika musu aljihunsu da kudade don a kakaba musu dan takarar da za su zaba.
''Muna da labarin cewa hadda kudade dalar Amurka da naira ana nan ana ba su. Kuma idan ana maganar siyasa ya kamata a bari mutane subi ra'ayin kansu.
Ina kira da babbar murya ga Shugaban jam'iyya Abdullahi Adamu da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, akan su duba su tausaya ma jam'iyyar APC a jihar Sokoto," in ji Isah Jabbi Usman.
Kimanin mutum 145 ne suka nuna sha'awar tsayawa takarar gwamna a karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulkin kasar.
Sai dai duk da rashin jituwa a wasu jihohin, ana sa ran zaben fid da gwanin zai gudana ba tare da wani rudani ba a wasu jihohin, musamman inda APCn ke rike da gwamnati kamar irinsu jihar Zamfara, da Yobe, da Borno, da Gombe da sauransu.
Kasa da mako guda kenan da itama babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta fara nata zabukan na fid da gwani a matakin yan majalisun jihohi da na tarayya, kuma jiya Laraba ta gudanar da na yan takarar gwamna.
Amma itama ba a kwashe lafiya ba a wasu jihohin, kamar jihar Zamfara inda tun kafin fara zaben wasu yan takara suka ce sun lura da yan matsaloli da suka sanyaya musu gwuiwa, a don haka suka sanar da batun shiga zaben.
Sai dai hakan bai hana gudanar da zaben ba, wanda daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar APC a baya da suka balle wato Dauda Lawal Dare, ya yi nasarar samun tikitin yi wa PDPn takarar gwamna a jihar.
Ko a jihar Kaduna babbar jam'iyyar adawar ta fuskancin zargin kyale wasu yan takara suka rika sayen kuri'ar deliget-deliget kan miliyoyin naira, wanda hakan ya yi sanadin wasu yan takarar fasa shiga zabukan da zargin cewa ba dimukradiyya ake yi ba.