Patricia Etteh: EFCC ta kama tsohuwar Shugabar Majalisar Wakilan Najeriya kan zargin rashawa

Etteh

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa a Najeriya, EFCC, ta kama tsohuwar Shugabar Majalisar Wakilan ƙasar, Ms Patricia Etteh.

Jaridun ƙasar sun ruwaito cewa EFCC ta yi awon-gaba da Ms Etteh ne kan zargin almundahanar kuɗaɗe a ma'aikatar raya yankin Neja Delta wato NDDC da yawansu ya kai naira miliyan 287.

Wata majiyar EFCC ta fada wa jaridar Punch cewa Ms Etteh ta karbi naira miliyan 130 daga kamfanin Phil Jin Project Limited da NDDC ta bai wa kwangilar naira miliyan 240 a 2011.

A kan haka a yanzu EFCC ta neme ta ta yi bayanin shigar kudin asusunta amma ta gaza fadar komai a kai.

''Etteh ba darakta bace ko yar kwangila, saboda haka me ya kai wannan kudi asusunta. Akan haka muke bukatar ta yi bayani kuma kawo yanzu bata yi ba," in ji majiyar.

An zabi Patricia Etteh a matsayin Shugabar Majalisar Wakilai a 2007, to amma ta yi murabus ne bayan 'yan watanni bisa zargin karkatar da wasu kuɗaɗe.

'Yan majalisa a lokacin sun yi barazanar tsige ta daga mukamin Shugabar Majalisar kafin ta yanke shawarar sauka da kanta.

A wancan lokacin ana zarginta da ware wasu makudan kuɗaɗe don bada kwangilar gyaran gidan da aka tanadar wa kakakin majalisa.

Ita ce mace ta farko a Najeriya da ta taba jagorantar majalisar a tarihi.

Kamen nata na zuwa ne kwana kaɗan bayan da EFCC ta cafke Akanta Janar na ƙasar, Ahmed Idris, bisa zargin sama da fadi da Naira biliyan 80.

EFCC ta ce ta kama shi ne bayan ya ki amsa gayyatar da ta yi masa don amsa tambayoyi.

Wasu 'yan Najeriya sun rika tsokaci kan kama Akanta Janar din da zargin wawushe biliyoyin, la'akari da cewa yana rike da babbar kujera a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da ke ikirarin yaƙi da cin hanci da rashawa.