'Yan Najeriya na yi wa gwamnatin Buhari shaguɓe kan kama Akanta Janar da EFCC ta yi

Ahmed Idris

Asalin hoton, OTHER

Lokacin karatu: Minti 2

An wayi garin Talata 17 ga watan Mayun 2022 ƴan Najeriya suna ta mayar da martani kan kamun da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon ƙasa wato EFCC ta yi wa Babban Akantan kasar, bisa zarginsa da almundahanar kuɗi har naira biliyan 80. 

Hukumar, a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce ta kama Ahmed Idris ne a ranar Litinin a Kano da ke arewacin kasar. 

EFCC na zargin Ahmed da karkatar da kuɗin ta hanyar amfani da abokansa da iyalai da sauran hanyoyi.

Ta ce an yi amfani da kuɗin wurin gina rukunin gidaje a Kano da Abuja.

An kama Ahmed Idris bayan ya ƙi amsa gayyatar da EFCC ta rinƙa aika masa domin tuhumarsa kan zarge-zargen da ake yi masa, kamar yadda hukumar ta bayyana.

Dandalin sada zumunta na Tuwita da Facebook sun zama manyan wuraren da ƴan ƙasar suka bazama suna bayyana ra'ayoyinsu a kan wannan lamari da ya kunno kai.

Maudu'ai biyar ne da suka danganci batun suke tashe a Tuwita da suka hada da #80bn da #Ahmed Idris da #EFCC da #Accountant General da kuma #ASUU, inda dubban mutane ke tattaunawa.

A dandalin Facebook kuwa kusan mutum 25,000 ne ke tsokaci kan batun da safiyar Talatar.

Mutane sun fi mayar da hankali ne wajen yi wa Shugaba Buhari shaguɓe tare da alaƙanta batun da yajin aikin da malaman jami'a ke yi a halin yanzu, wanda ya sanya ɗalibai zaman gidan tilas.

Yayin da wasu kuma suke ganin abin kunya ne a ce ana samun irin wannan lamari na almundahana a gwamnatin Buhari, wacce tun kafin kafuwarta ta dinga da'awar cewa za ta yi yaƙi da cin hanci da rashawa.

Ga dai abubuwan da wasu ke faɗa a Tuwita:

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

@LadyRoza_001 ta ce: "A ƙasar da ke fama da talauci, mutum ɗaya zai saci naira biliyan 80 cikin ƙasa da shekara huɗu da ɗarewarsa kan wannan muƙami. Wannan lamari ne mai muni."

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

@ifeanyidamian11 ya ce: "A yanayin da ake ciki da ɗalibai ke zaune a gida saboda yajin aiki tsawon wata biyu, amma wani mai son zuciyar ya sace naira biliyan 80, yayin da ita ASUU ke neman a biya ta abin da ko kusa da wancan kuɗin bai kai ba."

A shafin BBC Hausa na Facebook kuwa kusan mutum 3,00 ne suka yi tsokaci kan labarin.

Abdullahi Auwal Sulaiman ya ce: "A daidai lokacin da ASUU suke yajin aiki a kan biliyan 200, sai ga shi mutum daya kacal ya saci biliyan 80 shi kadai. Allah ya isar mana.

Abubakar Ambasador ya ce: "Kai jama'a! Wai su waye za su riƙe amana a wannan kasar de don Allah? Kowa ya samu dama kawai ya kwashe dukiyar ƙasa. Innalillahi Wa'inna Ilaihin Raji'un!

Hassan Yabour ya ce: "Wato dai kowa jira ya kai ya samu dama a Lanjeriya. Ya Allah ka da ka ba duk mai son satar kudin Lanjeriya damar samun mukami.