Sokoto: An rufe kwaleji a jihar bayan tarzoma kan zargin saɓo

Asalin hoton, UGC
'Yan sanda a jihar Sokoto da ke arewa maso gabashin Najeriya sun ce sun kama wasu matasa biyu da ake zarginsu da hannu a kisan da aka yi wa wata ɗaliba da aka zarga da yi wa Annabi Muhammadu S.A.W. ɓatanci.
Su ma shugabannin al'umma na ci gaba da yin tir da kisan ɗalibar.
A ranar Alhamis ne wasu ɗalibai da mazauna yankin suka yi wa wata ɗalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari duka sannan suka ƙona gawarta saboda zargin ta zagi Annabi a dandalin sadarwa na WhatsAPP. Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da ainahin abin da ya faru ba zuwa yanzu.
'Yan sanan Sokoto sun ce sun kama mutum biyu da ake zargi da aikata kisan.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar ya yi Allah-wadai da aikin mutanen da suka kashe ta, inda ya yi kira da a kama tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Wata sanarwa daga sakataren masarautar ta nemi mazauna jihar da su "kwantar da hankali" kuma "su zauna lafiya".
A nasa ɓangaren, shi ma babban malamin Kirista a Sokoto Bishop Mathew Hassan Kukah ya yi tir da aikin mutanen yana mai cewa "wannan ba shi da wata alaƙa da addini".
Cikin wata sanarwa da aka fitar a Sokoton, Kukah ya ce Musulmai da Kirista sun zauna cikin kwanciyar hankali tsawon lokaci.
"Wannan ba shi da wata alaƙa da addini. Kiristoci da Musulmai sun zauna tare cikin kwanciyar hankali tsawon lokaci a Sokoto. Dole ne a duba lamarin nan a matsayin babban laifi kuma dole ne doka ta yi aikinta," in ji shi.
Abin da ya faru tun farko
Rahotanni daga Jihar Sokoto a Najeriya na cewa wasu da ake zargin ɗalibai ne a kwalejin ilimi ta Shehu Shagari sun tayar da tarzoma bayan da aka zargi wata daliba da yin saɓo, abin da ya fusata ɗalibai suka shiga cinna wuta da hayaniya a makarantar.
Rahotanni sun ce har an yi asarar rayuka sakamakon wannan lamari, sai dai babu tabbaci daga hukumomi kan lamarin.
Tun bayan da aka soma wannan hayaniya aka tura sojoji da jami'an kwantar da tarzoma zuwa kwalejin ilimin domin kwantar da tarzomar.
Ko da BBC ta tuntuɓi rundunar yan sanda reshen Jihar Sokoto, mai magana da yawun rundunar ASP Sanusi Abubakar ya ce jami'an da suka tura sun kwantar da tarzomar kuma komai ya lafa.
Yadda lamarin ya faru
Wani ɗalibin kwalejin da BBC ta tuntuɓa ya bayyana cewa a lokacin da ɗaliban suka samu labarin faruwar lamarin, rigima sai ta kaure a cikin makarantar.
A cewarsa malamai da sauran shugabannin kwalejin sun yi ƙoƙarin su dakatar da ɗaliban daga wannan tarzoma amma abin ya ci tura, inda har jami'an tsaro suka je makarantar suna harba wa ɗaliban hayaƙi mai sa hawaye.
Ɗalibin ya bayyana cewa idan aka harba hayaƙin sai ɗaliban su ma su ɗauka su jefa wa jami'an tsaron. Ya ce ba ɗaliban kwalejin bane kaɗai suka tayar da hargitsin har da na waje suka shiga cikin kwalejin.
A cewarsa, wadda ake zargi da aikata saɓon an ɓoye ta a ɗakin jam'ian tsaro da ke ƙofar kwalejin inda masu tarzomar suka sha ƙarfin jami'an tsaron suka ɓalla ƙofar ɗakin suka ciro yarinyar.
Ya ce an yi ƙone-ƙone da farfasa muhimman kayayyaki a cikin kwalejin musamman motocin malamai.
Me jami'an tsaro suka ce
Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Sokoto ta tabbatar da faruwar wannan tarzoma sai dai ba ta yi ƙarin bayani kan abubuwan da suka faru ba inda suka ce suna gudanar da bincike.
ASP Sanusi Abubakar wanda shi ne mai magana da yawun ƴan sandan ya ce ƴan sandan tare da haɗin gwiwar wasu jami'an tsaro sun bazama a yankin kuma a yanzu akwai kwanciyar hankali.
Ya ce ba su da tabbaci kan maganganun da ake yi na cewa wasu sun rasa ransu haka kuma bai tabbatar da ko an kama wani daga cikin masu tarzomar ba.
Bugu-da-kari ASP Sanusi yace idan akwai wani karin bayani musamman daga binciken da suke yi za su sanar nan gaba.
Tuni dai hukumomin kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto suka sanar da rufe makarnatar har sai abin da hali yayi.











