Nama da kwari da aka kirkira a dakin bincike na kara lafiya da kare muhalli

    • Marubuci, Daga Helen Briggs
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC kan Muhalli.

Fara abinci da naman da aka kirkira a dakin gwaji hade da kwari ka iya zama wata hanyar kakkabe hayaki mai gurbata muhalli da samar da ruwa da kuma 'yantar da doron kasa daga lalacewa.

Wannan shi ne abin da masu bincike suka gano, ta hanyar tantancewar masana muhalli da suka bayyana hakan da fa'ida.

Masana kimiyya sun ce, takurawa kasa da ake yi da shuka abincin da muke ci da kashi 80 ka iya sauke mata nauyi, ta hanyar komawa cimakar da mutanen Turai ke ci.

Sai dai har yanzu ba a san ko masu saya za su sauya dabi'ar cin abincinsu.

An fara kokarin samar da abincin mai dauke da sinadaran protein da sauransu, yayin a bangare guda kuma ake alkinta kasa.

Masana kimiyya a Finland da sukai nazarin abinci mai gina jiki, sun gano yawancin wasu daga cikin irin abincin da muke amfani da su, na da kaso uku da ke takurawa muhalli; amfani da ruwa da kasa sai kuma hayaki mai gurbata muhalli.

Sun ce komawa amfani da nama da madara da sauran abincin da ake samu a jikin dabbobi, ka iya ragewa kasa nauyi da kashi 80 cikin 100, a bangare guda kuma ana kara samun nau'o'in abincin, da suka hada da dangin nama da ganyayyaki.

Amma sun gano wasu karin abubuwan da karamar fasaha ka iya taimakawa da su, da wadanda za su maye gurbin wadanda muke da su, ciki har da rage cin nama da maye gurbinsa da kayan lambu, hakan zai kare kasa.

"Idan aka rage cin naman dabbobi, da maye gurbinsu da tsirrai masu dauke da sinadarin protein, hakan zai sanya a samu raguwar dumamar yanayi, da rage amfani da kasa da ruwa," in ji Rachel Mazac ta jami'ar Helsinki.

Amma ta ce akwai kuma "kamanceceniya wajen killace kayan lambu da mutane ke ci a matsayin abinci. Idan kana bin ka'idar tsara lokacin cin abinci da nau'in da ya kamata ka ci, hakan zai kai kashi 75 cikin 100 na abincin da muke samu a jikin dabbobi".

Binciken da aka wallafa a mujallar Nature Food, ya yi nazari kan sabbin nau'o'in abinci da ake da tabbacin za su kasance wani bangare na rayuwarmu ta fuskar cimaka, wanda yawanci sun dogara ne kan fasaha kafin su tsiro, dabbobi da tsirrai na daga ciki.

Cikin kayan abincin da aka yi nazari a kai sun hada da:

  • Gyare da fara
  • Samar da ruwan kwai inda za a yi kiwon kajin a dakin gwaji
  • Nau'in ganyen mai yanayi da latus
  • Samar da sinadarin protein da aka samar daga malafar jaki ko mushrooms a turanci
  • Madara, nama, kayan marmarin berries da aka samar a dakin gwaji.

Dr Asaf Tzachor a jami'ar Cambridge, wanda ke cikin tawagar masu binciken, ya ce sakamakon binciken labari ne mai dadi da karfafa gwiwa, abin da ake bukata shi ne masu amfani da su ne kadai ya kamata su aminta da hakan, domin ana bukatar sauyi".

Bincike na baya da aka gudanar, ya nuna komawa amfani da tsarin yana da inganci ta fannin lafiya da kasa baki daya.

Wani rahoto na baya-bayan nan da wata hukumar da ke sa ido kan sauyin yanayi ta fitar, ya nuna komawa amfani da tsirrai kamar hatsi da kayan lambu, don amfani da madara da nama zai inganta lafiyar al'umma.