Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa ba a hukunta masu yin kalaman kiyayya a Indiya
- Marubuci, Daga Sharanya Hrishikesh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Delhi
Shin abu ne mai sauki ka wanye kalau idan ka yi kalaman kiyayya a Indiya?
Abin da ya faru a baya-bayan nan lokacin bikin Ram Navami da mabiya addinin Hindu suka yi a ranar 10 ga watan Afirilu ya alamta hakan. An gudanar da bikin na bana cike da kalaman kiyayya har da tashin hankali a wasu jihohin.
A kudancin jihar Hyderabad, wani dan majalisar jam'iyyar BJP da aka haramta wa amfani da shafin Facebook a shekarar 2020 saboda kalaman kiyayya da yake yi cikin waka da bakaken maganganu, ya ce duk wanda bai iya sunayen abin bauta Ram ba, za a kore shi daga kasar nan ba da jimawa ba.
Kwanaki kafin lokacin, wani bidiyon ya karade shafukan sada zumunta da ke nuna wani malamin addinin Hindu na ikirarin zai sace da kuma yi wa mata Musulmai fyade a arewacin jihar Uttar Pradesh. Amma 'yan sanda ba su yi rijistar batun ba sai bayan mako ɗaya, bayan bullar bidiyon da kuma tashin hankalin da ya biyo baya. Daga bisani a ranar Laraba aka kama shi.
A kusan wannan lokacin, wani malamin addinin Hindun Yati Narsinghanand Saraswati wanda aka bada belin sa, ya sake yin wani kalamin kiyayyar a wani taro a birnin Delhi, ya bukaci mabiya addinin Hindu su dauki makamai domin kare wanzuwarsu.
Ya yi kalaman a wani biki da 'yan sandan suka ce wadanda suka shirya shi ba su nemi izini ba, hakan ya take daya daga cikin ka'idojin da da aka gindaya kafin a ba da belin Mr Narsinghanand', amma babu wani mataki da aka dauka a kan sa.
Shekara da shekaru, kalaman kiyayya babbar matsala ce a Indiya.
A shekarar 1990, wasu masallatai a birnin Kashmir suka yi ta yada huduba kan kalaman kiyayya da ya tunzura mabiya addinin Musulunci masu rinjaye da ke tsaunin Kashmir. A dai wannan shekarar, shugaban jam'iyya mai mulki ta BJP, LK Advani, ya jagoranci wata tawaga domin gyaran wurin bauta da ke arewacin garin Ayodhya - lamarin da ya sanya mabiya addinin Hindu suka far wa wani tsohon masallaci abin da ya janyo tashin hankali a yankin.
Sai dai lamarin ya munana a cikin 'yan shekarun nan, sakamakon yadda 'yan Indiya ke jifan juna da kalaman kiyayya.
Karuwar shafukan sada zumunta da amfani da su da wadatar tashoshin talbijin da ke yada shirye-shirye kunshe da kalaman kiyayyar, da yadda 'yan siyasa ke wallafawa a shafukan sada zumuntar, wadanda ke ganin sassaukar hanya ce da za su yi fice, lamarin ya gagari hukumomi shawo kan illolin da hakan ke haddasawa, in ji masanin kimiyyar siyasa Neelanjan Sircar.
"Tun da fari, kalaman batanci na karuwa a lokacin zabe. Amma yanzu sauye-sauyen da aka samu, da ganewar da 'yan siyasa suka yi na amfani da kalaman kiyayya ga wani bangare da al'ummar mazabarsu ba sa ga-maciji da su wajen samun tikitin darewa mukamin da suke nema, don haka 'yan siyasa ke amfani da kalaman kiyayyar,'' in ji Sircar.
Kafar talbijin ta NDTV, wadda ta fara bibiyar kalaman kiyayyar da fitattun mutane suke yi daga shekarar 2009, an samu kalaman kiyayya da batanci da manyan 'yan siyasa kama daga ministoci da 'yan majalisu, suka yi ya wuce kima.
Wani rahoto da aka fitar a watan Janairu ya nuna irin wadannan kalamai sun karu tun bayan karbar mulkin jam'iyyar Firaminista Narendra Modi a shekarar 2014.
Ana zargin yawancin shugabannin jam'iyyar BJP mai mulki, ciki har da ministoci, da shallake tuhumar kalaman kiyayar da suka aikata. Ana zargin wasu daga cikin 'yan adawa kamar dan majalisa Asaduddin Owaisi da dan uwansa Akbaruddin Owaisi, da yin kalaman kiyayya.
Amma dukkansu sun musanta zargin, kuma kotu ta wanke Akbaruddin Owaisi ranar Laraba kan wasu zarge-zargen da suka shafi kalaman a shekarar 2012.
Kwararru sun ce Indiya na da isassun dokokin da za ta hukunta masu kalaman kiyayya.
''Sai dai zartar da dokar abu ne mai wuya. Yawancin lokuta, alkalan ba sa son yin shari'ar," in ji Anjana Prakash, babbar lauya waddda ta taba rubutu da rokon kotun koli ta dauki mataki da hukunta wasu daga cikin shugabannin addinin Hindu da suka yi kira ga mabiyansu su far wa Musulmi a watan Disambar bara a wani taro da aka yi a jihar Uttarakhand.
Indiya ba ta da takamaimaimiyar ma'ana guda kan kalaman kiyayya. Amma yawancin gundumomin Indiya sun haramta kalaman kiyayya, an kuma yi rubuce-rubuce da dokoki daban-daban kan wadanda aka samu da kalaman amma babu wani abin a-zo-a-gani da aka yi kan hakan.
Haka kuma, hatta abubuwan da ka iya tunzura mutane yin kalaman kiyayyar an haramta su, ciki har da nuna wariya, da wata ba'a da ta shafi ko kusanci da addini wadda da ka iya sosa zukatan mabiya addinin - duka an haramta su amma hakan bai hana mutane yi ba.
Lokuta da dama, ana kai kararrakin da suka shafi kalaman kiyayya gaban kotunan Indiya. Amma abin takaicin, alkalai ba sa daukar batun da muhimmanci, kuma a nan ake barin maganar.
A shekarar 2014, lokacin da ake sauraren wata kara a gaban kotun koli, an bukaci alkalin ya fitar da wasu bayanai da hukunce-hukuncen da aka tana da ga masu kalaman kiyayya musamman daga 'yan siyasa da malaman addinai, kotun ba ta dauki matakin ba.
Sanya doka ko haramci kan wani abu, abu ne mai sauki, amma zartar da hukuncin shi ne abin damuwa, saboda ba a iya daukar mataki akan fitattun mutane kama daga 'yan siyasa da shugabannin addinai da sauransu. A maimakon hakan, sai kotun ta bukaci hukumar shari'a, da wata hukuma mai zaman kan ta da ke sa ido kan harkokin gwamnati su yi nazari akain batun.
A rahoton da gwamanati ta fitar a shekarar 2017, hukumar ta yi bayanai kan wasu hanyoyin na daban da za a iya bi domin mafance matsalar, musamman wajen gabatar da jawaban da ke rikidewa na kiyayya.
Sai dai wasu kwararru sun nuna damuwa kan matakin.
"Amfanin dokar zai bada damar gano wadanda ke yin kalaman, da kuma tantance ainahin abin da ake nufi da kalaman kiyayya, da abin da za ka fada ya kai ga zama n kiyayyar," in ji Aditya Verma, lauya a kotun kolin Indiya.
Ya ce babbar damuwar, da aka samu jami'an gwamnati a ciki. Ya sanya misali da yadda 'yan sandan Birtaniya suka ci tarara manyan jami'an gwamnati ciki har da Fira Minista Boris Johnson - saboda take dokokin kullun korona.
Mr Verma ya kara da cewa: "Ta yiwu a samu wasu da za a yankewa hukuncin, amma abin damuwar shi ne an yi dokar, bare a sanya hukunci kan ?''
"Matukar ba a dauki matakin hukunta ko ma waye ya aikata kalaman kiyayyar ba, to babu abin da zai sauya.Ta yaya za a dinga yi wa doka hawan kawara?"
Akwai abubuwan da ke biyo bayan tashin hankalin da ya faru, sakamakon kalaman batancin da aka yi.
"Ya yin da ya kasance wurin da ka ke zaune ya zama wurin da ba ka farin ciki da shi, ba ka son zama a wurin, sannan ana yawan yin kalaman da ke harzuka mutane, mutane na daukar wannan tsokanar fada, mutane za su fara tsoron zuwa wurin ba tare da dalili ba,'' in ji Mr Sircar.
"Wannan shi ne ainahin abin da ke faruwa anan."