Ramadan 2022: Yadda Musulman Ukraine suke azumi da buda-baki a fagen yaki

Women gather to have their meal after a day of fasting

Asalin hoton, Niyara Mamutova

Bayanan hoto, Yin buda-baki lokacin Ramadan wani muhimmin abu ne da ke hada Musulmai wuri guda duk da yakin da ake ciki
    • Marubuci, Daga Swaminathan Natarajan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

"Ta yaya za a yi hankalinka ya kwanta a lokacin da kake jin karar jiniya a ko wane lokaci, ko lokacin da kake kallon hotunan makarantu, da asibitoci da gidaje da aka lalata?" Niyara Mamutova ta dasa ayar tambaya. "Ganin gawawwaki da konannun gidaje na saka ni cikin damuwa. Akwai matukar damuwa. Wannan watan na Ramadan cike yake da damuwa."

Niyara 'yar kabilar Tatar ce da ta tsere daga yankin Crimea bayan da kasar Rasha ta kwace shi a shekararar 2014. Wata Musulma 'yar kasar ta Ukraine daga birnin Kyiv Viktoria Nesterenko ta kara jaddada ra'ayin Niyara.

Matan biyu sun shaida wa BBC yadda suke fama da kalubalen yin azumin watan Ramadan a inda ya zama fagen yaki.

'Ina cike da damuwa'

"Ina ta yawan ganin munanan abubuwan da suka faru a yakin a cikin kwakwalwata," in ji Viktoria. "Fararen-hula da dama da suka hada da kananan yara sun mutu a hannun sojojin kasar Ukraine a kusa da birnin Kyiv. Wannan watan na Ramadan sam bana jin alamun yanayi mai tsarkakewa, cike nake da damuwa."

Viktoria Nesterenko with a man in military uniform

Asalin hoton, Viktoria Nesterenko

Bayanan hoto, Viktoria Nesterenko tana taimaka wa sojoji da fararen-hula ta hanyar kungiya mai zaman kanta

Kalilan daga cikin al'ummar kasar Ukraine ne ke bin addinin Musulunci - za a iya cewa kashi 1 bisa dari, kamar yadda alkaluman da ba na hukuma ba suka nuna.

Amma kuma Musulman kasar sun zaku suna jiran watan Ramadan bayan da suka yi kewarsa na shekaru biyu sakamakon annobar korona. Yaki ya daidaita shirinsu na wannan shekarar.

"Abu mafi matukar wahala shi ne ka tsara kasancewarka cikin yanayi na ibada da koyon darasi. Ina bukatar karanta Alkur'ani mai girma sosai kana in mayar da hankali na wajen ibada. Yana da mattukar wahala ka mayar da hankali sosai wajen yin sallah da addu'oi saboda galabaita da damuwa,'' in ji Viktoria.

Niyara na shayar da jaririya, don haka ba ta azumi, amma Viktoria tana yi. Duka suna fuskantar kalubalen mayar da hankali kan ibada.

"Ko shakka babu muna samun lokaci mu yi sallah. Lokacin yaki an amince da wasu abubuwa a gare mu. Za a iya hada salloli - sallar azahar da la'asar ko sallar yamma da ta magariba. Ta wannan hanya za mu iya cika ayyukanmu na addini," ta kara bayyanawa.

'Babu inda ke da kwanciyar hankali'

A cikin shekaru takwas, Niyara na zaune a kudu masu gabashin garin Zaporizhzhia. Tana da wata kungiya mai zaman kanta da ke tafiyar da ayyuka da dama daga fadakarwa game da muhalli zuwa yaki da nuna wariya ga Musulmai.

Niyara Mamutova with her four children

Asalin hoton, Niyara Mamutova

Bayanan hoto, Niyara (rike da jaririya) ta bar iyalanta mako uku bayan soma yaki

Yakin ya fara makonni uku kacal bayan da ta haifi danta na hudu, a daidai lokacin da iyalanta ke tunanin yin gyara da kawata gidansu saboda watan Ramadan.

"Mun razana matuka. Makamai masu linzami na fadawa a kan filin sukar jiragen sama, wuraren ajiyar mai na kamawa da wuta …Dakarun kasar Rasha na kara dannowa cikin birnin. Don haka muka yanke shawarar ficewa."

Ba kamar a yankin Crimea ba, wanda kusan babu zub da jini, wannan mamayar akwai zub da jini mai munin gaske.

Don haka iyalan suka kara gaba, wannan karon zuwa birnin Chernivtsi a yammacin Ukraine don samun mafaka. Akwai matukar wahala ga 'ya'yanta.

"Ya'yana sun rabu da abokansu. Sun rasa gidansu. Ba mu da kwanciyar hankali a wannan birnin. Makamai masu linzami da bama-bamai za su iya fadawa cikin ko wane birni a Ukraine."

Tuna baya

Muslim men praying in a mosque

Asalin hoton, Niyara Mamutova

Bayanan hoto, Masallatai da dama a Ukraine suna karbar 'yan gudun-hijira

Da farko sun nemi mafaka a cikin wani masallaci amma daga bisani sun samu sun kama haya a wani wuri. Kawa-zuci da tunanin abubuwan baya na watan Ramadan na tuna mata da abubuwan da ta rasa.

"Duka iyalan mun saba yin azumi tare, da sallah tare, da kuma yin buda-baki tare. Yanzu iyalanmu sun rarrabu saboda yakin. Wasu sun bar kasar kana suna kasashen daban-daban. Ba yanayi ne na farin ciki ba,'' Niyara ta kara bayyanawa.

Mijinta na aiki a matsayin limami a wani masallaci wanda wani gida ne da aka sauya wa fasali.

Akwai dokar hana fitar dare a birnin Chernivtsi, da hakan ke nufin dole a wasu lokutan mijinta ya kasance a masallaci idan ya bata lokaci. Amma Niyara ta samu sabbin kawaye a wannan wuri da ba ta saba da shi ba.

"Muna haduwa da sauran Musulmai mu yi buda-baki. Muna taimakon juna. Muna kuma yin kira ga Musulmai masu hali da ke nan su bayar da gudumawar abinci ga wadanda suka asa matsugunansu.''

Karancin naman halal

A ko wace rana tana taimakawa wajen dafa abinci ga mutanen da suka rasa matsugunansu da ke zaune a cikin masallaci.

A plate of traditional meal

Asalin hoton, Niyara Mamutova

Bayanan hoto, Karancin abincin halal matsala ce ga mata

"Muna dafa kusan duka na'ukan abinci amma ba ma samun naman halal a nan. Akwai dai wasu naman kaji na halal," in ji Niyara.

Ta ce kungiyoyin tallafawa Musulmai a kasashe kama su Turkiyya na samar da abinci kana Musulman yankin na samar da kwanuka da tukwane da sauran kayayyakin da ake bukata wajen yin girkin.

Viktoria na amfani da daskararren nama da kifi wajen shawo kan matsalar.

"Muna kokarin samar da abincin halal. Amma yanzu muna da matsala ta karancin naman halal. Musulmai da ke cikin kauyuka na da matsalar samun daskararen nama."

Kafin a fara yakin tana aiki ne a matsayin darakta a cibiyar tantance abincin halal ta Halal Certification Centre a birnin Kyiv. Tana cike da fatan za a shawo kan matsalar karancin abincin halal ba da jimawa ba.

Tallafa wa yaki

Musulmai maza da mata na cikin bataliyar rundunar sojin Ukraine. Wasu ba su dade da kafa kungiyoyin masu rike da makamai na sa-kai ba. "Dangina da kawayena na fafatawa a kasar Russia," a cewar Viktoria.

Viktoria Nesterenko with armed soldiers

Asalin hoton, Viktoria Nesterenko

Bayanan hoto, Viktoria tana samar da abinci ga sojoji da fararen-hula

"Muna samar da agajin jin kai, da taimakawa wajen kwashe mutane, da tara kudade da kuma sayen kayan aiki wa sojojinmu."

Babban masallacin a birnin Kyiv na da kashi biyar bisa dari kacal na yawan mabiyansa da aka sani, abin da ya bata wa Viktoria rai.

Tana ganin har yanzu akwai Musulmai a cikin birnin da ke gudanar da muhimman ayyuka ko kuma a sansanonin soji suna sallah a masallaci.

"Ina ganin dole in cigaba da aiki tare da taimaka wa mutane iya karfina. Ina da nauyin da ya rataya a kai na a matsayina na 'yar kishin kasa. Karfin mutanen Ukraine na tattare da hadin kai - dole mu zama tsintsiya madaurinki daya kana mu taimaki juna. Ita ce kadai hanyar da za mu iya samun galaba a kan abokan gabarmu."

Jarabta da kuma tawakkali

Niyara na cike da fatan cewa addininta zai taimaka mata wajen cin jarrabawar wannan lokaci na ibtila'in rayuwa da ya same ta.

Men praying in a mosque

Asalin hoton, Alina Smutko

Bayanan hoto, Musulman Ukraine da dama sun shiga aikin soja ko kuma aikin sa-kai

"Addinina na da matukar muhimmanci a daidai wannan lokaci mai tsanani, Yana ba ni karfin guiwa. Yana ba ni amsoshin tambayoyi. Ka kan fahimci cewa yakin wata jarabtar ce."

Amma Niyara ta yi amanna cewa Allah ne ya ba ta karfin guiwar jure wa wannan matsala.

"Muna rayuwa, tare da yin addu'oi da kuma jiran dawowar zaman lafiya," ta bayyana.