Yaƙin Ukraine: Putin ya sauya tsarin duniya - amma ba yadda yake so ba

Mutane na wuce katon allo dauke da hoton shugaba Putin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar 10 Maris, an kafa wani allo mai hoton shugaba Putin a Simferopol da ke yankin Crimea, inda aka rubuta "Rasha ba ta fara yaki, maimakon haka kawo karshensa ta ke yi"
    • Marubuci, Daga Allan Little
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC

Mamayar da shugaba Vladimir Putin ya yi a Ukraine ta sauya duniya baki dayanta. Ana rayuwa a sabon karni mai cike da hadari, kwatankwacin shekarun cacar baka da zamanin da aka kawo karshen bangon Berlin.

1px transparent line

Ba safai ake rayuwa a lokutan da aka yi wa tarihi hawan kawara ba, da tunanin abin da zai je ya komo, har kuma a fahimci halin da ake ciki.

A watan Nuwanbar 1989, ina tsaye cikin dusar kankara a dandalin Wenceslas da ke Prague, babban birnin kasar wanda a wancan lokacin ake kira Czechoslovakia. Ina kallon yadda ake shirin haifar da sabon karni na duniyarmu.

Al'ummar gabashin Turai ta yunkuro domin kare kanta da kuma kawo karshen mulkin danniya. An ruguza katangar Berlin, kana an samar da wani sabon yanki a Turai a wancan lokacin.

A birnin Prague, marubuci kuma mai bayyana sabanin ra'ayi, Vaclav Havel ya yi wa dandazon mutum 400,000 jawabi, daga farfajiyar wani gini mai hawa biyu. Zuwa yammacin wannan ranar aka raba gwamnatin kwamunusanci ta kasar da mulki, kuma cikin makonni Havel ya zama shugaban kasar karkashin tafarkin mulkin dimukradiyya.

Daga wannan lokacin na fara yin nazari kan yadda duniyar ke sauyawa, wanda lokaci ne mai cike da tarihi - inda akan idonka kana ganin yadda duniya ke sauyawa cikin sauri.

Vaclav Havel lokacin da ya ke yi wa dandazon dubban mutanen da suka taru a dandalin Wenceslas da ke Prague, 24 Nuwamba 1989

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Vaclav Havel a dandalin Wenceslas na Prague, ranar 24 Nuwamba 1989

Shin sau nawa ne cikin tarihin Turai, tun bayan juyin juya halin Faransa aka samu irin wannan sauyin? Ina ganin kamar sau biyar haka ta taba faruwa. Wannan na shekarar 1989, shi ne karo na shida.

Sai dai irin wannan lokacin da ake sake samar da sabuwar duniya, yayin juyin juya halin da suka faru na baya-bayan nan da shugaba Putin ya kaddamar, wato na mamayar Ukraine ta amfani da karfin soji, shi ne ya dawo da zamanin baya da abubuwan da suka faru a shekarun da suka shude.

Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz ya bayyana wannan lokaci a matsayin mai matukar wahalarwa - yayin da sakatariyar harkokin wajen Birtaniya Liz Truss ta ce wannan "gagarumin" yanayi na sauyi ne. Ta kuma ce zamanin yin sakaci ya wuce har abada.

line

Muhimman lokuta a tarihin nahiyar Turai

Kutsen kurkuku,14 Yuli 1789

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Afka wa kurkukun Bastille na ranar 14 ga watan Yuli 1789
  • 1789: Juyin-juya halin Faransa. An kawo karshen mulkin mulaka'u, tare da samar da jamhuriya
  • 1815: 'Yan majalisar Vienna sun zana sabuwar da taswirar Turai, da daidaita rabon madafan iko, da kuma tabbatar da zaman lafiya a gwamman shekaru bayan yakin zamanin Napoleon
  • 1848: Juyin-juya halin na masu sassauci a kasashen Turai wadanda suka kafa mulkin dimukradiyya
  • 1919: Yarjejeniyar Versailles. Sabbin kasashe masu cin gashin kai sun maye gurbin tsofaffin dauloli
  • 1945: Yalta - kasashe mafi karfin iko sun amince a raba Turai zuwa bangaren yammaci Turai da na yankin Soviet. Daga nan ne "labulen karfe" ya tsaga nahiyar gida biyu
  • 1989: Dimukradiyya ta bayyana a tarayyar Soviet da kasashen gabashin Turai. Shekara biyu bayan nan tarayyar Soviet ta durkushe. Vladimir Putin ya kira lokacin "yanayi mafi muni a karni na 20"
line

A baya-bayan nan, Quentin Sommerville daya daga cikin ma'aikatan BBC da ya goge wajen dauko rahotanni a wuraren da ake yaki, ya ce ruwan bama-baman da Rasha ta yi a birnin Kharkiv na Ukraine: "Idan ba ka san irin wannan dabarar yakin ba, to tabbas ba ka taba mai da hankali akan abin da ke faruwa a duniya ba ke nan."

Alamu da shaidu sun dade da bayyana kan abin da Rasha ke son yi.

Shekaru 20 ke nan tun bayan da ya tura sojoji zuwa Georgia, tare da ikirarin yana taimakon 'yan awaren kasar ne.

Daga bisani, ya aike da 'yan leken asiri zuwa wasu biranen Birtaniya dauke da guba domin hallaka 'yan Rasha da suka tserewa kasar.

A shekarar 2014, ya mamaye gabashin Ukraine, tare da mallakar yankin Crimea.

Duk da wannan, Jamus da yawancin kasashen Turai, sun yi biris tare da dauke ido saboda sun dogara ne da makamashi da iskar gas din da Rasha ke sayar musu.

Shekara guda bayan mamayar yankin Crimea, suka amince da gina wani dogon bututun da zai bunkasa safarar iskar gas tsakanin Rasha da kasashen Turai.

Wani lamari da Liz Truss, ta bayyana a matsayar babbar matsalar da kasarta ke fuskanta.

Birtaniya ta zama tudun mun tsira inda Rasha ke adana kudadenta, tun zamanin Firaminista John Major.

Manyan attajiran Rasha sun tara biliyoyin daloli a Birtaniya, tare da sayen gidaje masu matukar tsada, da kuma jiragen sama, da mu'amala da manyan 'yan siyasa da attajirai da bayar da tallafi ga kungiyoyin agaji.

Tambayoyi kalilan aka yi kan ta ina suke samun irin wadannan mahaukatan kudaden, kuma cikin lokaci kadan.

Bututan mai 2, a kusa da Lubmin a Jamus , watan Maris 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bututan mai biyu, a kusa da Lubmin a Jamus

Da fari, ya yi amanna kasashen turai na cike da tarin matsaloli, ya shaida hakan a lokacin da aka samu rarrabuwar kawuna tsakaninsu. Kan zaben shugaba Donald Trump da ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai ya tabbatar da hasashen na shi.

Sai kuma tasowar masu ra'ayin sassauci a kasashen Poland da Hungary, hakan ya kara sanyawa ya samu kwanciyar hankalin cikar muradunsa.

A shekarar 1992, 'yan asalin Sabiya sun kaddamar da yaki domin karyawa da kassara sabuwar kasar da ta samu 'yancin kai, ko mu ce jaririya wato Bosnia. Sun yi ta musun cewa Bosnia ba ta da wani tushe na ta na kashin kai, sannan sun kafe cewa ba ta da wani cikakken tarihi da har za a bata gashin kai, sannan sun kafe tabbas wani bangare ne a kasar Sabiya.

Wannan shi ne ainahin kallon da Shugaba Vladmir Putin ke yi wa Ukraine.

A Bosnian special forces soldier and civilians come under fire from Serbian snipers, Sarajevo, 6 April 1992

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani sojan kundumbala na Bosniya tare da fararen hula na boye wa wani mai harbinsu dan Sabiya a birnin Sarajevo, ranar 6 ga watan Afrilun 1992

A 1994, yayin da yakin Balkan ke kara ruruwa, gabashin Turai na fuskantar abubuwan da ke tafe - kuma kowace kasa ke fatan samun rayuwa da 'yar uwarta cikin lumana.

Sai dai babu wanda ya san ko za su sami damar shiga kungiyar tsaro ta NATO.

An yi wata muhawara a lokacin, kan ko ya dace kasashen da suka balle daga tarayyar Soviet na iya kafa wata kungiyar tsaro ta uku domin ta zama shinge tsakanin NATO da Rasha.

Rasha ta kasance maras karfin fada a ji a shekarun 190, kuma kasashen gabashin Turai ba su amince cewa Rasha za ta dade cikin wannan hali na rashin karfin fada a ji ba, shi yasa suka nemi shiga kungiyar NATO.

A karkashin mulkin shugaba Bill Clinton, Amurka ta ci gaba da kokarin fadada kungiyar ta NATO. Shugaba Boris Yeltsin ya fusata matuka da ya gano wannan shirin na Amurka - na shigar da wasu kasashen gabashin Turai cikin kungiyar ba tare da ta tuntubi Rasha ba.

US President George HW Bush with Boris Yeltsin in Maryland, US, 1992

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Amurka George HW Bush da takwaransa na Rasha Boris Yeltsin sun gana a Maryland a 192

Ko Boris Yeltsin zai iaya mayar da kasa kamar Rasha ta zama kasa ta zamani kamar na yammacin Turai? A farkon shekarun 1990 ya fara mayar da kasar bisa tafarkin mulki irin na kasashen yammacin Turai.

Sai dai ba da dadewa a 1998, sai gwajin da yake yi ya rikito. Tattalin arzikin kasar ya fado kasa sosai, takardar kudin kasar ta Rouble ta rasa kashi biyu cikin uku na darajarta cikin wata guda sannan hauhawar farashi a kasar ya kai kashi 80 cikin 100.

People queue in front of a Russian bank, Moscow, September 1998

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dogon layin masu neman karbar kudi a gaban wani bankin Rasha a binin Mosco cikin watan Satumbar 1998
Presentational white space

Yawancin 'yan Rasha ba su ji dadin yadda wannan gwajin ya talauta su ba, kuma sun dauka wata dabara ce ta azurta masu mulkinsu kuma a talauta sauran 'yan kasar.

Wannan ne ya sa Rasha ta ja baya daga wannan tsarin kuma ta koma bisa tafarkin mulki na shekarun baya - wato na kasa mai shugabannin da ke da cikakken iko, mai nuna ikonta kan kananan kasashen da ke makwabtaka da ita.

Tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Zbigniew Brzezinski ya taba cewa Rasha na da zabin zama mai bin tafarkin dimokradiyya, ko kuma ta bi tafarkin mulkin kama karya, amma babu yadda za ta iya hada duka biyun a lokaci guda.

Palace Square and Winter Palace at dusk, St Petersburg, Russia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fadar Hunturu da yammaci a birnin St Petersburg na Rasha
1px transparent line
The crenellated red walls of the Kremlin in Moscow

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hoton Fadar Kremlin inda ake iya ganin jar katangar fadar da ke birnin Moscow

Duk yadda abubuwa suka kasance, tilas abubuwan da ke faruwa su shafi kowa.

Amurka da Tarayyar Turai sun raba duniya gida biyu. Dukkan kasashen da suka ci gaba da yin huldar kasuwanci da Rasha za su fuskanci fushin kasashen yamma - kuma za a daina damawa da su daga yanzu.

Wannan ya haifar da wani sabon labulen karfe ke nan amma na tattalin arziki - wanda a yanzu ya raba Rasha da kasashen yamma.

Akwai kuma rawar da China ke takawa bayan wannan juyin-juya halin. China da Rasha sun hade wuri guda saboda kiyayyar da suke da ita kan karfin fada a jin da AMurka ke da shi tsakanin kasashen duniya da kuma da amannar da suka yi cewa babban kalubalen da za su fuskanta nan gaba zai fito ne daga kasashen yamma da ke kara hadewa karkashin tutar dimokradiyya.

Vladimir Putin and Chinese leader Xi Jinping meet in Beijing, February 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Vladimir Putin da Shugaban China Xi Jinping sun gana a Beijing a Fabrairun 2022

Wasu masu nazarin kasar China na cewa za ta yi kokarin kalubalantar mamayar da dalar Amurka ta yi a kasuwancin duniya ta hanyar mayar da takardar kudinta ta yuan a matsayin wadda duniya za ta iya komawa kan ta idan ba ta son amfani da dalar Amurkar.

Wannan yakin da Putin ke yi na iya sauya taswirar tattalin arzikin duniya, kuma zai hana Amurka daukan matakin ladabtarwa kan China nan gaba.

Amma babban abin lura a nan shi ne - wannan yaki ne tsakanin kasashen da ke bin tafarkin dimokradiyya da wadanda ke bin tsarin mulki na kama karya.

Sannan wannan yaki ne tsakanin yadda wasu ke kallon yadda ya dace a rika gudanar da dangantaka tsakanin kasashen duniya.