Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
EFCC ta kama tsohon gwamnan Anambra Willie Obiano
Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta kama tsohon gwamnan Jihar Anambra Willie Obiano.
Ta kama shi ne a ranar Alhamis, sa'o'i bayan ya miƙa mulki ga sabon gwamnan jihar Charles Soludo.
Mai magana da yawun hukumar ta EFCC Wilson Uwajaren ya tabbatar wa BBC da kamen inda ya ce yana ofishinsu na Legas.
Rahotanni dai sun ce EFCC ta kama shi ne a filin jirgin Legas a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Jihar Texas ta Amurka.
Mitsa Uwajaren ya bayyana cewa dama tuni suna haƙon Mista Obiano domin yana cikin jerin mutanen da suke son kamawa amma ba su da damar kama shi sakamakon rigar kariyar da yake da ita a lokacin yana gwamna.