Wasu 'yan Najeriya na cewa haƙurin da Buhari ya bayar bai isa ba

    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 3

Bayan shafe fiye da wata 'yan Najeriya na fama da matsalar ƙarancin man fetur, wasu 'yan ƙasar na cewa haƙuri da neman afuwar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi bai isa ba.

Mafi yawan ma'abota shafukan BBC Hausa da suka bayyana ra'ayoyinsu ba su gamsu da kalaman shugaban ba, suna masu cewa "kayan masarufi ma sun yi tsada".

Buhari ya bai wa mutanen kasar hakuri kan matsalar rashin wuta da wahalar fetur da ake fama da su cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

"Gwamnatinmu na aiki ba dare ba rana domin ganin an kawo karshen wannan matsala. Kuma shirin da aka tsara a farkon wannan wata za a aiwatar da shi domin tabbatar da an kawo karshen karancin man da ake fama da shi," in ji shi.

Wani mai suna Abbas Mustapha: "Mu ci hakuri mu mutu. Mun saba jin irin wannan daga gare shi. Ina da tabbacin 'yan Najeriya sun fi kowa hakuri a duniya."

'Kayan masarufi ma sun yi tsada'

Mutum sama da 4,000 ne suka yi martani kan labarin neman afuwar da BBC Hausa ta wallafa a shafinta na Facebook, da kuma wasu fiye da 600 a Instagram. Kazalika, mutum kusan 90 ne suka yi tsokaci a Twitter ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Cikin saƙon da Buhari ya wallafa, shugaban ya taɓo abubuwa kamar rashin wutar lantarki na baya-bayan nan da kuma dogon layin da 'yan Najeriya ke hawa kafin su sayi man fetur, yana mai cewa ya umarci kamfanin mai na NNPC ya ɗauki dukkan matakin da ya dace.

"Kuma na bayar da umarni ga ma'aikatar man fetur da albarkatun kasa da NNPC da sauran jami'an tsaro su ɗauki mataki kan duk waɗanda aka kama da laifi."

Sai dai wani ma'abocin shafin BBC a Twitter ya tuna wa shugaban cewa kayan masarufi ma fa sun ƙara tsada, sannan kuma ƙungiyar ASUU na yajin aiki.

"Kayan masarufi ma sun yi tsada. ASUU ma suna yajin aiki. Gwamnoni da dama ba sa biyan albashi, wasu kuma suna zabtare albashin. Ga matsalar tsaro, ga na cin hanci da rashawa. Ko Shugaba Buhari ya manta da su?"

Shi kuwa wani da ya kira kan sa Northerner cewa ya yi "mun haƙura" tare da addu'ar Allah ya kawo ƙarshen lamarin.

Shi kuma wannan shawartar Buhari ya yi da ƙoƙarta ya koma Najeriya don fuskantar ƙalubalan da ke gabansa.

Ita kuwa Maryam Shanono cewa ta yi "mun yafe baba".

Wahalhalu biyar da 'yan Najeriya ke ciki a wannan lokaci