Shugaba Buhari ya bai wa 'yan Najeriya hakuri kan wahalar fetur da rashin wuta

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa mutanen kasar hakuri kan matsalar rashin wuta da wahalar fetur da ake fama da su.

Cikin wata sanarwa da shugaban ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce ba ya jin daɗin halin dogon layin da 'yan kasar ke ciki na man fetur, "wani abu da gwamnatinmu ta yi kokarin kawarwa cikin shekaru bakwan da muka yi a ofis".

Ya kara da cewa hakuri ne da ake bai wa duka sassan Najeriya baki daya.

Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da matsalar rashin wuta da ci gaba da fuskantar wahalar man fetur a Najeriya.

"Gwamnatinmu na aiki ba dare ba rana domin ganin an kawo karshen wannan matsala. Kuma shirin da aka tsara a farkon wannan wata za a aiwatar da shi domin tabbatar da an kawo karshen karancin man da ake fama da shi," in ji sanarwar.

Shugaban ya ce suna aiki tare da kungiyoyin yan kasuwa irinsu MOMAN da masu dakon man irinsu IPMAN domin dai ganin an fita daga wannan hali.

Za a ci gaba da kawo isasshen mai a ko wacce jiha kamar yadda ake yi a baya, domin kawo karshen layin da ake fama da shi a fadin kasar.

Duk da cewa ana fama da matsalar koma baya a kasuwar makamashi ta duniya a wadannan watannin, kuma gwamnati za ta yi abin da za ta yi domin tabbatar da cewa masu amfani da man masu samu matsalar farashin man da ake fama da shi a duniya.

"Na samu labarin cewa wasu mutane da yawa na abubuwan da ba su dace ba a defo-defo na dauko mai ciki har da masu gidajen mai.

"Kuma na bayar da umarni ga ma'aikatar man fetur da albarkatun kasa da NNPC da sauran jami'an tsaro su dauki mataki kan duk wadanda aka kama da wannan ta'ada", in ji Buhari

Game da matsalar wutar lantarki da aka samu a fadin kasa kuwa, Shugaba Buhari ta cikin sanarwar ya ce an shawo kan wannan matsala.

"Raguwar wutar da aka samu na da alaka da sauyin yanayin da bukatar da ke karuwa wanda ya zo daidai da matsalar na'urori da muka samu a tashar wutar.

"A kan haka kuma muna aiki babu dare babu rana domin shawo kan wannan matsala, domin tabbatar da samu wutar lantarki isasshiya," kamar yadda ya ce.

Ya ƙara da cewa "An dauki mataki tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar wutar lantarki d NNPC da zai taimaka a samu megawat 1,000.

"Ya zuwa yanzu an samu nasarar dawo da megawat 375 na wutar bayan gyara wani bututun gas mai mahimmanci da aka yi.

"Ina farin cikin sanar da cewa an amince da ba da dala miliyan 50 domin shigo da gas domin tabbatar da samu da kuma dorewar megawat 800 na wutar lantarki a Najeriya.

"Ba ni da shakkar cewa hakan zai kawo karshen wannan matsalar da muke ciki a kusa.