Rasha ta ce ba za ta taba yafe kalaman da Shugaba Biden ya yi kan Putin ba

Asalin hoton, Getty Images
Fadar gwamnatin Rasha ta mayar da martani da kakkausar murya tare da yin Allah-wadarai da kiran da Shugaban Amurka Joe Biden ya yi wa Shugaba Putin da cewa mai mummunan laifin yaki ne, inda fadar ta Kremlin ta ce magana ce da ba za ta taba yafewa ba.
Kalamin, wanda shi ne suka mafi kaushi da Biden ya yi a kan takwaran nasa na Rasha, ya kasance ne bayan da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya nemi taimako daga Majalisar Dokokin Amurka.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan ne karon farko da Shugaba Biden ya kira shugaban na Rasha a matsayin wanda ya aikata laifin yaki, inda daga baya kuma ya biyo da wani sako na tuwita, wanda a cikinsa yake bayyana irin abin da ya kira mummunar ta'asa da barnar da ya ce Putin na aikatawa a kan Ukraine.
Sakatariyar yada labarai ta Fadar Gwamnatin Amurkar, White House, Jen Psaki a wani taron manema labari ta kare kalaman na Shugaba Biden:
Ta ce, ''Kalaman Shugaban, a zahiri suke karara. Yana magana ne ta gaskiyar abin da ke zuciyarsa saboda abin da ya gani a talabijin, wanda ayyuka ne na dabbanci, da mugun dan kama-karya ya aikata hanyar mamayar wata kasar waje.''
Ms Psaki ta kara da cewa akwai matakin shari'a a kan hanya, wanda zai ci gaba da kasancewa kan hanya a Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka.
Mataki ne da za a ci gaba da sabuntawa a kai-a kai.
Shi ma kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurkar Ned Price, ya jaddada goyon baya ne ga kalaman na Shugaba Biden.
Yana mai cewa "Idan kana maganar gaskiya, magana a matsayinka na dan-Adam, kana ganin irin abin da muke gani, wadannan munanan hotuna a talabijin, harin Rasha a kan asibitin haihuwa a Mariupol, da hare-hare a kan gine-ginen, da makarantu, da unguwannin farar hula, abu ne mai wuyar gaske ka kasa bayyana wadannan kalamai.
A martaninta fadar gwamnatin Rasha ta zargi Shugaba Biden da furta kalaman da ta ce ba za a yafe ba, tare da zargin Amurka da kisan dimbin jama'a a fadin duniya.

Asalin hoton, AeroVironment Inc.
Tun da farko shugaban na Amurka ya yi alkawarin bayar da karin tallafin soji na dala miliyn 800 ga Ukraine, yana mai cewa, Mista Putin zai dandana kudarsa a kan miyagun abubuwa.
Mista Biden ya ce Amurka za ta samar da makamai masu lalata igwa da na kariyar sama da kuma jiragen sama na yaki marassa matuka ga gwamnatin Ukraine.
Ya kuma yi gargadin cewa yakin na Ukraine da Rasha ka iya tsawaita da kuma wuya.
Yayin da duk ake wannan shi kuwa Shugaba Volodymyr Zelensky, na Ukraine a jawabinsa na bidiyo na baya-bayan nan, ya ce yana da cikakken kudurin ci gaba da tattaunawar zaman lafiya da Moscow.











