Ukraine: Daliban Najeriya da suka yi tafiyar awa 72 don ficewa daga Ukraine

Asalin hoton, Getty Images
Har yanzu mutane da dama na ci gaba da barin yankunan Ukraine saboda irin aman wutar da Rasha ke yi a wasu yankuna na ƙasar.
Mata da maza, yara da manya har ma da tsofaffi wasu ma har da dabbobinsu ne ke tsere wa rikicin Ukraine da Rasha.
'Yan Najeriya ma musamman dalibai wadanda karatu ya kai su can na daga cikin wadanda ke guje wa tashin hankalin na Ukraine.
Daliban Najeriya da dama sun koka a kan irin halin da suka tsinci kansu saboda rikici tsakanin Rasha da Ukraine da kuma irin bakar azabar da suke fuskanta a hanyarsu ta barin inda don neman mafaka.
Wasu daga cikin daliban na Najeriya sun shaida wa BBC irin bakar wuyar da suka sha kafin su samu mafaka.
Sarhan Mustapha Salim, na daga cikin irin wadannan dalibai na Najeriya, ya ce duk da yake a yanzu ya isa Budapest a Hungary bayan ya taso daga yanin Dnipro na Ukraine, ya fuskanci bakar wuya kafin ya isa.
Ya ce," Sai da muka shafe sama da sa'oi 72 kafin mu isa Budapest, don mun shafe kwana uku a hanya, amma kuma Alhamdulillah ba tafiyar kafa muka yi ba".
Sarhan, ya ce a kan hanya bai fuskanci matsaloli ba, a Dnipro ya fi fuskantar matsala musamman wajen shiga jirgin kasa saboda akwai cunkoson mutane gashi kuma babu tikiti.
Dalibin ya ce, saboda rashin tikitin wajen shiga jirgin kasa idan ya zo sai mutum ya yi da gaske zai samu shiga.
Sarhan Mustapha Salim, ya ce yanzu sun gode wa Allah domin jami'an Hungary sun karbe su har an ba su masauki amma kuma ba su kai ga tuntubar jami'an diplomasiyyar Najeriya a Hungary ba.
Shi ma wani dalibi mai karatun aikin Likita a Ukraine din, wanda ya ke zaune a Lviv da ke iyaka da Poland, ya shaida wa BBC cewa, harin farko da Rasha ta kai ma yana cikin wani asibiti da yake koyan aiki.
Ya ce," Bayan na idar da sallar asuba sai naji wucewar jirgin sama, ashe ba jirgi bane, missile ne wato makami mai linzami ne da ya wuce ta saman asibitin".
Dalibin ya ce bayan an kai harin sai suka yi kokarin kwashe marassa lafiyar da ke asibitin don sun kai kusan 200.
Karin bayani
Dalibai da dama na Najeriya dai sun fantsama kasashen da suke gani suna makwabtaka da inda suke a Ukraine domin guje wa rikicin Ukraine kuma cikin kasashen da daliban na Najeriya suka shiga kuwa akwai Romania.
Kuma tuni ofishin jakadancin Najeriyar a Romaniya ya shaida wa BBC cewa a ranar Laraba ne, yake sa ran isar jirgin saman da zai fara kwashe 'yan ƙasar zuwa gida.
A ranar Litinin ne, gwamnatin Najeriya ta ce daga Laraba ne za ta fara kwaso 'yan ƙasar waɗanda yaƙin Ukraine ya tilasta musu barin ƙasar zuwa maƙwabtan ƙasashe.
Da farko dai wasu 'yan Najeriyar ciki har da dalibai da ke Ukraine suka koka da irin cin zarafinsu da ake a iyakar Poland ga kuma azabar sanyi, abin da Gwamnatin kasar ta yi Allah-wadai da shi.
Hakan ya sa ma'aikatar harkokin wajen Najeriyar ta shawarci 'ƴan kasarta da ke barin ƙasar Ukraine da su nufi iyakar Hungary ko Romania, maimakon ƙoƙarin shiga ƙasar Poland don gujewa cin zarafi.
Gwamnatin Najeriya dai ta ce akwai 'ƴan kasarta kusan 4,000 a ƙasar Ukraine, galibinsu ɗalibai.
Ba daliban Najeriya ne kawai ke fuskantar tashin hankalin ba wajen neman mafaka a kasashen makwaftan Ukraine, dalibai da sauran jama'a ma haka suke.










