Rikicin Ukraine: Ofishin jakadancin Najeriya a Romania ya bai wa 'yan kasar '200' masauki

Mutanen da suka tserewa rikicin Ukraine

Asalin hoton, Reuters

Ofisoshin jakadancin Najeriya a ƙasashen da ke maƙwabtaka da Ukraine na ci gaba da karɓar 'yan ƙasar da ke ficewa a dai-dai lokacin da yaƙi ke kara rincaɓewa.

Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce tana aiki da ofisoshin jakadancin ƙasashen Ukraine da Poland da Rasha da Romania da kuma Hungary don tabbatar da ganin an mayar da su gida.

Bayanai sun ce ɗaruruwan 'yan Nijeriya ne suka tsallaka kan iyakar Ukraine, inda ake sa ran kwashe su zuwa birane mafiya aminci, kafin mayar da su Najeriya.

Romania ta kasance daya daga cikin kasashen da suka karbi 'yan Najeriya da ke zaune a Ukraine.

Jakadiyar Najeriya a Romania Safiya Nuhu, ta shaida wa BBC cewa, ya zuwa yanzu sun karbi 'yan Najeriya 200 inda suke kyautata zaton za su samu fiye da haka.

Ta ce," Bisa la'akari da cewa Najeriya tana da dalibai da dama a Ukraine, don haka mun san cewa dole a samu karin mutanen da za su shigo kuma mu a shirye muke mu karbe su don taimaka".

Jakadiyar ta ce," Ni 'yan Najeriyar da na karba a kasar da nake yi wa jakadanci sun ji dadi da irin karbar da aka yi musu ba kamar a wasu kasashen da wasunsu suka je basu ji dadi ba".

A Romania duk dan Najeriyar da ya shiga an karbe shi sosai, domin an basu wajen sauka wato makwanci, da abinci da layin waya da kuma abubuwan kariya daga cutar korona, in ji Ambasada Safiya Nuhu.

Ta ce, dama Romania ta yi alkwarin cewa duk wanda ya shiga kasarta daga Ukraine za a karbe shi ba tare da la'akari da ɗan wacce kasa bace.

Jakadiyar Najeriyar, ta ce dangane da batun ranan da za a fara mayar da 'yan Najeriyar zuwa gida, "a yanzu za a fara tantance adadin 'yan Najeriyar da suka shiga Ukraine tukunna, sannan a kiyasta wadanda ake tsammanin shigowarsu".

Ta ce." Nan bada jimawa ba za mu sanar da ranar da za su fara komawa gida, kuma da abin da sauki saboda mafi yawancin 'yan Najeriyar da ke Ukraine din dalibai ne, iyayen wasunsu sun taimaka sosai domin sun biya wa 'ya'yansu kudin jirgi tuni suka koma gida Najeriya".

Ambasada Safiya Nuhu, ta ce, hakan da iyaye suka yi ya yi matukar taimaka musu saboda an rage yawan wadanda ke zaune na jiran komawa gida.

Ta ce iyaye su kwantar da hankalinsu in dai har 'ya'yansu ko 'yan uwansu sun isa Romania to za a dawo da su gida domin suna nan suna kokarin yadda za a yi su da gwamnatin Najeriya.

Karin bayani

Hukumomi a Najeriya na shawartar 'yan ƙasar su tsallaka ƙasashen Poland da Hungary masu maƙotaka da Ukraine tun bayan Rasha ta fara kai hare-hare.

'Yan Afirka da ke kokarin tserewa daga Ukraine dai na korafi a kan wahalar da suke fuskanta da wariyar da ake nuna musu wajen tsallaka iyakokin kasa zuwa kasashen Turai makwabta.

Akwai tawagar dalibai da suka ce sun makale a iyakar Prezemysl da jami'an Ukraine ke gadi, saboda an hanasu wucewa.

A karshen mako ne ofishin jakadancin Najeriya a Poland ya ce ya aike ma'aikata kan iyaka domin taimaka wa 'yan kasarta tsallaka iyakar domin samun mafaka.