Rikicin Ukraine: 'Yan Afrika da ke son barin Ukraine na cikin tsaka-mai-wuya

Asalin hoton, Reuters
'Yan Afirka da ke kokarin tserewa daga Ukraine na korafi kan wahalar da suke fuskanta da wariyar da ake nuna musu wajen tsallaka iyakokin kasa zuwa kasashen Turai makwabta.
Wata 'yar Najeriya Ruqqayya da ke karatun likita a jami'ar Kharkiv ta shaida wa BBC cewa ta yi tafiyar sa'a 11 cikin dare domin isa Medyka-Shehyni, da ya haɗa iyaka da Poland, sai dai an hanata wucewa.
Ta ce ''na iske baƙaƙen fata na bacci a kan titi, kuma jami'an tsaro a kan iyaka sun umarce ni da na tsaya saboda 'yan Ukraine ake bai wa fifiko. Na rasa gane idan jami'an tsaron 'yan Ukraine ne ko Poland.
Ta shaida cewa a kan idonta ta shaidi yada ake cika motocin bas da turawa fararen fata, ana basu damar tsallake iyaka, yayinda adadin 'yan Afirka da bai taka kara ya karya ba kawai ke samun wannan dama bayan shan dogon-layi.
Ruqayyah na kokarin isa Warsaw domin ta hau jirgin sama da zai maidata gida Najeriya, wanda tuni ta saye tiketinta.
Isaac ma ya isa iyakar Medyka tun da misalin karfe 4:30 na safe amma sai aka sanar da shi a kan iyakar cewa 'yan Ukraine da Turkawa ake bari su soma wucewa kafin 'yan Afirka.
Akwai tawagar dalibai da suka ce sun makale a iyakar Prezemysl da jami'an Ukraine ke gadi, saboda an hanasu wucewa.
Daya daga cikinsu Timothy wanda ke karatun likitan a Lviv, kuma mamba ne kuma a kungiyar dalibai 'yan Najeriya a Lviv, ya ce ba a nunawa 'yan Ukraine irin wannan wariyar.
Shima Segun, wanda dalibi ne a Kyiv ya ce yana fargabar barin birnin saboda fasfo dinsa na hannun ajent din da ya sama masa bisar karatu.
"Bana iya yaransu idan kuma na ce zan tafi ban san ina za su ajiye ni ba, ko ina zan nufa," a cewarsa.
Karin haske
A jiya Asabar ofishin jakadancin Najeriya a Poland ya ce ya aike ma'aikata kan iyaka domin taimawaka 'yan kasarta tsallaka iyakar domin samun mafaka.
Wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta fitar ta shawarci 'yan Najeriya su shiga Poland ta kan iyakoki huɗu tsakaninta da Ukraine.
"Ma'aikatan jakadancin Najeriya da masu aikin sa-kai na nan suna jira da motoci don kwashe 'yan Najeriya a kan iyaka," a cewar sanarwar mai ɗauke da adireshin da ta ce 'yan Najeriya su nuna wa jami'an kan iyaka idan sun ƙarasa.
Tun ranar Alhamis Najeriya ta ce za ta shirya aikin ceto na musamman amma daga baya ta ce ba za ta iya ba har sai an buɗe filayen jiragen sama na Ukraine.
Ministan Harkokin Waje na Najeriya Geoffrey Onyeama ya ce ya gana da jakadun Ukraine da Rasha a Abuja babban birnin ƙasar.











