Rikicin Ukraine : Najeriya ta fusata da cin zarafin ɗalibanta a iyakar Poland

Bayanan bidiyo, Bidiyo: Ana wulakanta mu ƴan Afirka a Ukraine ana nuna bambanci
    • Marubuci, Daga Stephanie Hegarty
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnatin Najeriya ta yi Allah-wadai da rahotannin da ke cewa an hana ƴan ƙasarta, da na wasu kasashen Afirka ficewa daga kasar Ukraine da ke fama da mummunan yaƙi.

Wani ɗan Najeriya Isaac da ke ƙoƙarin shiga ƙasar Poland ya ce ma'aikatan kan iyaka sun shaida masa cewa ba aikinsu ba ne kula da ƴan Afirka.

"An fatattake mu, an riƙa ture mu da ƙotar ƴan sanda da dukanmu da sanduna," kamar yadda ya shaida wa BBC.

Shi ma ofishin harkokin wajen Afirka ta Kudu ya ce ci zarafin ɗailiban a kan iyaka.

Haka kuma an samu rahotanni da dama da ke cewa jami'an tsaron Ukraine sun hana ƴan Afirka hawa motocin bas da jiragen ƙasa da ke zuwa kan iyaka.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

1px transparent line

Osemen wani ɗan Najeriya, ya shaida wa BBC cewa ya yi ƙoƙarin shiga jirgin ƙasa a Lviv don kai shi kan iyakar Poland amma aka ce ƴan Ukraine ne kawai za a ba su izinin shiga.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce akwai ƴan Najeriya kusan 4,000 a ƙasar Ukraine, galibinsu ɗalibai.

Ya ce sau da dama ana hana wata tawagar ƴan Najeriya tsallaka wa Poland, don haka ala tilas sai koma wa Ukraine suka yi, don sake shirya sabuwar tafiya zuwa Hungary.

"Duk wanda ke ƙoƙarin tsere wa rikici na da haƙƙi irin na kowa, yana da ƴancin wucewa kamar yadda dokokin Majalisar Ɗinkin Duniya suka yi tanadi, don haka bai kamata a ce launin fatarsa ko kuma bambancin fasfonsa ya sa a riƙa nuna masa bambanci ba", in ji Shugaba Buhari, cikin wani saƙo da ya wallafa a Twitter.

Fiye da 'yan Ukraine 350,000 ne suka yi nasarar tsere wa mamayewar Rasha ya zuwa yanzu.

'Otel don ƴan Ukraine kawai'

Kafin fara rikicin an yi imanin cewa akwai dubban ɗalibai ƴan Afrika da ke karatu a ƙasar Ukraine

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kafin fara rikicin an yi imanin cewa akwai dubban ɗalibai ƴan Afrika da ke karatu a ƙasar Ukraine

Wata ɗalibar jami'a Ruqqaya, ƴar Najeriya tana karatun likitanci a birnin Kharkiv da ke gabashin ƙasar lokacin da aka kai hari a birnin.

Ta yi tafiya ta tsawon sa'o'i 11 cikin dare kafin ta isa mashigar Medyka tare da Poland.

"Lokacin da na zo nan akwai baƙaƙen fatar da na tarar suna kwana a kan titi," kamar yadda ta shaida wa BBC.

Ta ce masu gadi ɗauke da makamai ne suka gaya mata cewa ta jira tun da ya zama dole a bar ƴan kasar ta Ukraine su fara wucewa tukunna.

Ta ƙara da cewa ko da ta kalli motocin bas ɗin, sai ta ga fararen fata kawai ake bai wa damar shiga ta kan iyaka, yayin da ƴan Afirka ƙalilan ne kawai aka zaɓo daga cikin jerin gwanon mutanen da suka taru.

Bayan ta shafe awanni da yawa, daga karshe aka ba ta izinin wucewa ta nufi Warsaw don koma wa Najeriya.

Ita ma wata ɗaliba mai suna Asiya ƴar Somalia da ke laƙantar ilimin likitanci a wata jami'a da ke babban birnin Kyiv, ta ce irin haka ta faru a kanta lokacin da ta isa Poland, ta ce an gaya mata "Ƴan Ukraine kawai ke da damar sauka a otal ɗin.

Rundunar ƴan sandan Poland ta shaida wa BBC cewa duk wanda ke gudun hijira a Ukraine ana maraba da shi zuwa Poland ba tare da la'akari da ko ɗan wacce ƙasa ba ne.

BBC ta yi ƙoƙarin tuntuɓar sojojin kan iyakar Ukraine amma har yanzu babu wata amsa daga gare su.

Ministan harkokin wajen Najeriya Geofrey Onyeama, ya ce ya tattauna da takwaransa na Ukraine Dmytro Kuleba, kuma an ba su tabbacin cewa an bai wa jami'an tsaron kan iyakokin Ukraine umarnin barin duk wani baƙo da ke barin Ukraine damar wucewa ba tare da wani sharaɗi ba.

Yanzu haka ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta shawarci ƴan kasarta da ke barin ƙasar Ukraine da su nufi iyakar Hungary ko Romania, maimakon ƙoƙarin shiga ƙasar Poland.

Jakadan Najeriya a Romania ya shaida wa BBC cewa kawo yanzu kimanin ƴan Najeriya 200 ne akasarinsu ɗalibai suka isa Bucharest babban birnin ƙasar daga Ukraine.

Wata ɗaliba da yanzu haka ke Bucharest ɗin Safiya Nuhu ta ce wasu da dama na ci gaba da zuwa.

Map
line