Za a yi zaɓen shugaban Najeriya ranar 25 ga Fabarairun 2023

Hukumar zaɓe a Najeriya INEC ta sanar da jadawalin babban zaɓe na 2023, inda za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa ranar Asabar 25 ga watan Fabarairun 2023.

Shugaban INEC Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Asabar.

Kazalika, za a gudanar da zaɓen 'yan majalisun tarayya tare da na shugaban ƙasar.

Zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi zai gudana ranar 11 ga watan Maris na 2023 ɗin.

A cewarsa, an zaɓi ranar ce saboda a tabbatar an yi aiki da sabuwar dokar zaɓe, wadda ta tanadi cewa wajibi ne a bayyana ranar zaɓen aƙalla kwana 360 kafin kaɗa ƙuri'a.

Ya ƙara da cewa hukumar za ta wallafa sauran tanade-tanaden dokar zaɓen "a lokacin da ya dace".

Sauran ranakun da suka shafi babban zaɓen:

  • 28 ga Fabarairu 2022: Wallafa ranakun gudanar da zaɓe
  • 4 ga Afrilu zuwa 3 ga Yunin 2022: Gudanar da zaɓen fitar da gwani na jam'iyyu da kammala sauraron ƙorafe-ƙorafe
  • 10 zuwa 17 ga Yunin 2022: Aika sunayen 'yan takarar shugaban ƙasa da 'yan majalisar tarayya ga INEC ta shafinta na intanet
  • 1 zuwa 15 ga Yulin 2022: Aika sunayen 'yan takarar gwamna da 'yan majalisar jiha ga INEC ta shafinta na intanet
  • 28 ga Satumban 2022: Fara yawon kamfe na 'yan takarar shugaban ƙasa da 'yan majalisun tarayya
  • 12 ga Oktoban 2022: Fara kamfe na 'yan takarar gwamna da 'yan majalisar jiha
  • 23 ga Fabarairun 2023: Kammala kamfe na 'yan takarar shugaban ƙasa da 'yan majalisar tarayya
  • 9 ga Maris na 2023: Kammala kamfe na 'yan takarar gwamna da 'yan majalisar jiha