Pakistan: 'Yan sanda na neman bokan da ya caka wa mace ƙusa a tsakar kanta

Asalin hoton, Peshawar Police
Jami'an 'yan sanda na neman wani mai magani ruwa a jallo a Pakistan bayan da aka ce ya caka ma wata mata mai juna biyu ƙusa a ka.
Matar ta kai kanta wani asibiti a Peshawar bayan ta yi ƙoƙarin cire wata ƙusa mai tsawon inci biyu daga kanta da filaya.
Tun farko ta gaya wa likitoci cewa ita ta caka wa kan nata ƙusar, sai dai daga baya ta shaida musu cewa wani mai magani ne ya yi wannan aika-aikar.
Ta kuma ce mai maganin ya yi ma ta alkawari cewa aikin zai tabbatar ta haifi ɗa namiji.
'Yan sanda sun ƙaddamar da bincike bayan da hoton asibiti ya bayyana a shafukan sada zumunta suna nuna yadda ƙusar ta huda kan matar.
Dakta Haidar Khan wanda likita ne a asibitin Lady Reading, ya ce matar "na nan cikin hayyacinta sai dai tana cikin azaba" yayin da ta isa asibitin.

Asalin hoton, Lady Reading Hospital
Mista Ahsan ya kuma ce jami'ansa za su binciki dalilin da yasa ma'aikata asibitin ba su sanar da ƴan sanda lamarin ba bayan da matar ta je asibitin.
Ma'aikatan lafiya a asibitin sun shaida wa jaridar Dawn ta yankin cewa matar ta ziyarci wani mai magani ne bayan da ta sami labarin irin aikin daga wani maƙwabcinta.
Sun ƙara da cewa matar mai ƴaƴa mata uku ce, kuma mijinta ya yi barazanar sakin ta idan ta sake haifar masa wata ƴa mace.
"Watanta uku da samun ciki amma saboda fargabar abin da mijinta zai yi, sai ta je wajen mai maganin," kamar yadda ma'aikatan lafiyan suka shaida wa jaridar Dawn.
A wasu ƙasashen yammacin Asiya, ana kallon ɗa namiji a matsayin wanda zai fi iya kawo wa gidansu arziki, a maimakon ƴaƴa mata, matakin da ke haifar da ire-iren waɗannan miyagun halayen daga mutanen da ke ikirarin su "masu magani ne".
Irin waɗannan masu maganin na da yawa a wasu yankunan Pakistan, musamman a yankin arewa maso yammacin kasar.
Cikin wani saƙon Twitter da ya wallafa, shugaban ƴan sandan Peshawar Abbas Ahsan ya ce wasu zaratan 'yan sanda "za su tabbatar da an gurfanar da mai maganin bogin wanda ya yi wasa da rayuwar wata mata kuma ya caka ma ta kusa a kanta bayan alkawarin karya da yayi mata cewa za ta haifi ɗa namiji."
Ƴan sandan sun shafe kwanaki suna yi wa ma'aikatan asibitin tambayoyi, baya ga kokarin da suke yi na gano inda matar ta ke, wadda ta bar asibitin bayan da ma'aikatan asibitin suka cire ma ta kusa daga kan nata.
"Nan ba da jimawa ba za mu damke matsafin," inji Mista Ahsan.











