Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gambia: An rantsar da shugaba Barrow na Gambia a karo na biyu
Shugabannin Afirka da dama ne suka halarci bikin rantsar da Adama Barrow yau a sabon wa'adin mulki na biyu tsawon shekara biyar.
An yi bikin ne a filin 'yancin kai na Bakau.
Shugabannin ƙungiyar ECOWAS irinsu Muhammadu Buhari, na Najeriya wadanda za su halarta, sun yi uwa da makarɓiya wajen mayar da Gambiya kan tafarkin dimokraɗiyya a 2017 bayan tsohon shugaba Yahya Jammeh, ya ƙi karɓar kayi lokacin da ya faɗi a zaɓen ƙasar.
An yi bikin lafiya saɓanin rantsuwar kama aiki ta farko lokacin da aka samu jinkiri sanadin ƙin amincewar Yahya Jammeh, ya sauka daga mulki.
Adama Barrow shi ne shugaba na uku da Gambiya ta gani tun bayan samun 'yancin kai a 1965.
Tuni 'yan kasar suka nuna fatansu a kan shugaban inda wasunsu ke bukatar a inganta bangaren ilimi, wasu bangaren lafiya, wasu kuma fatansu shi ne a samar musu titina da kuma saukar da farashin kayayyakin masarufi.A jawabin farko bayan sake zaɓensa a farkon watan Disamba, shugaba Adama Barrow, ya bayyana aniyar sabuwar gwamnatinsa na sake fasalin tsarin mulkin Gambiya, wanda zai iyakance wa'adin shugaban ƙasa.
An samar da tsarin mulkin ƙasar na yanzu a 1997, farkon mulkin kama-karya na tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh, wanda ya shafe shekara 22 a kan karaga.
A cewarsa, sabon tsarin mulkin zai kuma sake fasalin tsarin zaɓen ƙasar ta yadda zai ƙunshi batun zuwa zagayen zaɓe na biyu, idan ba a samu ɗan takarar da ya lashe kashi 50 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa ba.
Adama Barrow, mai shekara 56 ya lashe zaɓe a karo biyu ne bayan ya samu kashi 53 cikin 100 a ƙarƙashin tsarin cin zaɓe da ƙanƙanin rinjaye.