Zamantakewa: Lalacewar mu'amalarmu a shafukan sada zumunta

Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.

A wannan kashi na 26 din, shirin ya yi duba ne kan zamantakewar shafukan sada zumunta.

Shafukan sada zumunta masu abin tsiya da na kirki. Sabon dandalin baje kolin zamantakewarmu a wanan zamanin kenan. Can yini, can kwana, 24/7 in ji Bature.

Sai dai kuma duk da dabdalar da muke shafe lokaci muna yi a shafukan sada zumunta kamar ba mu faye bai wa hakkokin zamantakewar dandalin muhimmanci yadda ya kamata ba.

Zagi da cin mutunci da habaici da fariya da karya da dagawa da kece reni da fankama da cin zarafi da roko, kai har ma da gaba babu wanda aka bari a wannan sahar.

Kai wani cin mutuncin da za a yi maka watarana sai ya goge maka hadda ma.

Tamkar dai wasu na manta cewa hisabi fa ba a zamantakewar zahiri kawai zai tsaya ba, ko zamantakewar shafukan sada zumunta na abin da ka rubuta da wanda ka kalla ma akwai hisabi a kansa.

Filin ya ji ta bakin wasu masu yawan amfani da shafukan sada zumunta kan yadda ya kamata mu kyautata zamantakewarmu a wannan sahar, kuma sun ba da shawarwari.

Sai dai duk da wadannan matsaloli, akwai kuma tarin alkhairai na kafafen sada zumuntar.

Misali kana koyon darasi a fannonin rayuwa daban, da iya zama da mutane da ma sanin halayyar dan adam da samun labarai da koyon ilimi mai dumbin yawa daga wajen malamai da masu sharhi da ma sauran mutane.

Uwa uba kuma ana iya samun abokai na gari har a kulla zumunci mai dorewa kamar yadda Muhammad da Amina suka gaya min.

Wasu na baya da za ku so ku gani

Wasu karin abubuwan da za a kiyaye a ganina sun hada da kamewa da kauwacewa cin mutuncin mutane da dagewa kan sai an yarda da fahimtarka, kar ka bi mutane har shafinsu ka ci mutuncinsu a kan ra'ayinsu, gara ka garzaya naka shafin ka bayyana ra'ayinka.

Idan status din wance bai miki ba don a ganinki ta fiye saka shirme, to toshe ta zai fi a ce kin je kin ja ta da fada, idan kuma ka gane cewa kai wane yake yi wa habaici to toshe ka daina ganin status da story dinsa kawai.

Idan kuma ha haƙƙaƙe kai ne ke jawowa kanka zagi ta hanayr wallafa abubuwan da ba su dace ba, me zai hana ka yi kokarin daina wallafa su?

Abu na karshe mafi muhimmanci, shi ne gujewa bakin duniya ta hanyar fadar abin da ba shi kenan ba.

Sannan ku dinga kokarin tattaunawa da likitocin lafiyar kwakwalwa da masana halayyar dan adam don ba ku shawarwarin da suka dace akai-akai, don in ba haka ba, ina tabbatar muku watarana za a iya haukata tunanin wani a wannan sahar.

Kar dai a manta, hisabi fa ba a zamantakewar zahiri kawai zai tsaya ba, ko zamantakewar social media na abin da ka rubuta da wanda ka kalla ma akwai hisabi a kansa.