Tarayyar Turai ta farga da kasancewar sojojin haya na kamfanin Wagner a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

A makon nan ne Kungiyar Tarayyar Turai ta sanya takunkumi a kan kamfanin Wagner, wato wani kamfanin sojojin haya na Rasha da ake zargi da take hakkin dan adam a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ma wasu kasashe.

Tarayyar Turai ta ce ta daina horar da sojojin gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya saboda alakarsu da Wagner.

A Afirka, mayakansu na ayyuka a Libya da Sudan da kuma Mozambique sannan akwai yiwuwar suna aiki ma a Mali.

Me yasa sojojin kamfanin Wagner ke aiki a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya?

Sojojin na kasar ne domin taimaka wa Shugaba Faustin-Archange Touadéra, a yakin da yake da 'yan tawaye wadanda ke iko da bangarori da dama na kasar duk da fadadawar da gwamnati ke yi wajen murkushe su.

Kasar na fama da rikici tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba François Bozizé a shekarar 2013.

Mr Touadéra, wanda ya hau mulki a 2016 bayan zabe, na fama da yadda zai murkushe 'yan tawaye duk da kasancewar dakarun Faransa da na Majalisar Dinkin Duniya.

Gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta yi amanna cewa sojojin hayar Rashan na samun nasara a yakin da ake da 'yan tawayen.

An yi amanna cewa sojojin hayar kamfanin Wagner sun fara aiki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya tun a 2017, tun bayan da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da sojojin Rasha su bayar da horo a kasar.

A shekarar 2017, shugaba Touadéra, ya je Rasha domin sanya hannu a wasu yarjejeniyoyin tsaro tare da gwamnatin Rasha.

Yarjejeniyoyin sun hadar da taimakon soji inda za a yi ban gishiri in ba ka manda wato Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya za ta bai wa Rasha daiman (diamond) da zinare da kuma yureniyom (uranium).

Majalisar Dinkin Duniya dai ta amince ne da tura sojojin Rasha 175 domin su je su horar da na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Duk da cewa jami'an Rasha na musanta zarge zargen da ake musu, ciki har da na Tarayyar Turai a kan alakar sojojin haya na kamfanin Wagner da Rasha.

Masu sharhi sun ce yarjejeniyar da aka kulla ta bai wa kamfanin Wagner damar fara aiki a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

Tun daga wancan lokaci sojojin hayar kamfanin suka kasance a kasar mai albarkatun ma'adinai.

Gwamnatin Rasha ta ce ta tura sojoji masu horaswa zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ba tare da makamai ba, sannan kuma dukkansu ba su wuce 550 ba.

Kwararru a Majalisar Dinkin Duniya, sun yi amanna cewa akwai sojoji masu bayar da horo dubu biyu da Rasha ta tura Jamhuraiyar Afirka ta Tsakiya ciki har da wasu da ta dauka aiki daga Syria da kuma Libya inda mayakan kamfanin Wagner ke aiki.

Menene takamaimai abin da ake zargin sojojin Wagner da aikatawa?

Sojojin hayar kamfanin Wagner da na gwamnati na aikata fyade da yi wa fararen hula fashi a kauyukan kasar in ji Majalisar Dinkin Duniya da kuma Faransa.

A cikin wani rahoto da aka fitar a watan Agusta a kan take hakkin dan adam a Jamhuriyar Afirka Tsakiya, Majalisar Dinkin Duniya ta tattara korafi fiye da 500 daga watan Yulin shekarar 2020, ciki har da kisan gilla da azabtarwa da cin zarafi ta hanyar lalata.

A watan Oktoba,wata tawagar kwararru a Majalisar Dinkin Duniya ta ce wadanda sojojin Rasha suka kama ba a yi musu hukunci ba, kuma an kama su ba tare da aikata wani laifi ba, mutanen sun shigar da kara kuma har kawo yanzu babu abin da aka yi wanda hakan ke nuna cewa za a ci gaba da take hakkin dan adam a kasar.

A farkon watan ne kuma ministan shari'a na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Arnaud Abazene, a karon farko ya yarda cewa sojojin Rashar na take hakkin dan adam.

Yayin da kuma ya ce yawancin abubuwan da suka faru 'yan tawaye ma sun taka rawa, wannan shi ne karon farko da wani daga gwamnatin kasar ya amince sojojinsu da abokanansu na cin zarafin fararen hula.

Me ya sa Tarayyar Turai ta yanke hukuncin daukar mataki?

Mai magana da yawun tarayyar Turan, Nabila Massralli, ta shaida wa BBC cewa taron Brussels ya farga da cewa sojojin kamfanin Wagner na yin abin da suka ga dama , sannan irin abubuwan da ke faruwa a Jamhuriyar Afirka Tsakiya kuma ana zargin sojojin Wagner din da aikatawa..

Wani bincike da BBC ta yi, ya gano cewa sojojin Wagner sun kashe fararen hula da fursunoni a Libya tare da ɗana abubuwan fashewa.

A yanzu Tarayyar Turai ta ce ba ta goyon bayan ayyukan sojojin hayar kamfanin Wagner musamman a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Mecece alakar sojojin Wagner da kuma gwamnatin Rasha?

A hukumance ba bu wani abu, to amma akwai zargin da ake cewa akwai alaka.

Daya daga cikin wadanda tarayyar turai ta sanyawa takunkumi shi ne Valery Zakharov, wani tsohon mamba a ma'aikatar tsaron Rasha kuma mai ba wa shugaba Touadéra shawara.

A cewar tarayyar turai, Mr Zakharov, na daga cikin jiga jigai a kamfanin Wagner.

Sojojin Wgner sun yi suna a 2014, lokacin da suka yi yaki da 'yan awaren Rasha a rikicin gabashin Ukraine, tun daga wancan lokaci sojojin ke aiki a gabas ta tsakiya da kuma kasashen tsakiya da na kudancin Afirka.