Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da mutane suka fi tambayar Google a 2021
Shafin matambayi-ba-ya-ɓata ya bayyana jerin abubuwan da aka fi yayi, abin da ke alamta irin yadda shekarar 2021 ta kasance ga al'ummar duniya.
Katafaren kamfanin fasahar shi ne mafi shahara a shafukan da ke bayar da damar neman amsar kowace irin tambaya kuma duk shekara yakan fitar da abubuwan da aka fi tambaya da maudu'ai.
Shekara mai tsauri
Yayin da annobar korona rata sassan duniya, mun shiga 2021 tare da maudu'in 'doomscrolling', wata kalmar Ingilishi da ke nufin "ganin labarai marasa daɗin ji".
Maudu'in na bayyana yadda masu amfani da shafukan zumunta ci gaba da latsa wayoyinsu da zimmar ganin ƙarin labarai marasa daɗi.
Google ya ce an tambayi 'doomscrolling' fiye da koyaushe a faɗin duniya, inda abin ya fi yawa a watan Janairu.
Lokaci ne na rashin tabbas a faɗin duniya da zaƙuwa. An kulle iyakoki, an hana jirage tashi sannan an saka dokar kulle.
Mutane sun dinga hawa intanet don sanin me ke faruwa game da annobar ta korona kuma da yawansu sun nemi abin da ke damun su ne - "doomscrolling".
Lalurar ƙwaƙwalwa
A 2021, an duba kalmar 'mental health' wato 'lalurar ƙaƙwalwa' fiye da kowane lokaci biyo bayan shafe shekara guda cikin kaɗaici da kuma alhinin rashin 'yan uwansu da korona ta kashe.
Mutanen duniya sun yi ta tambayar 'yadda za a yi jinyar lalurar ƙwaƙwalwa' da kuma 'ta yaya za a warke?' fiye da kowane lokaci a baya.
Wani ƙarin dalili da ke nuna lalurar ƙwaƙwalwa ta dame mu a 2021, maudu'ai kamar 'body positivity' (lafiyar jiki) da 'affirmations' (tunani mai kyau) sun fi shahara sama da kowane lokaci.
Sauyin yanayi
Ba maganar lafiyar jiki kawai ake ba, lafiyar duniyarmu ma na damun mu.
Daga Guguwar Ida zuwa yunwa da kuma gobarar daji - duniya ta shaida tasiirin sauyin yanayi.
A cewar bayanan Google, mun duba hanyoyi mafiya tsafta na rayuwa fiye da kowane lokaci. 'Yaya za a alkinta' da 'rayawa' na cikin abubuwan da muka fi nema a shafin.
Mazauna birane da tsaunuka sun nemi bayanai kan 'tasirin sauyin yanayi' fiye da koyaushe.
Abin da bai ba da mamaki ba shi ne, ƙasar Fiji wadda sauyin yanayi ya fi yi wa illa, ita ce aka fi yawan nema.
Harkokin kuɗi
Mutane sun firgice game da ayyukansu da kuma tattalin arzikinsu, akasari saboda rashin tabbas da annobar korona ta haddasa.
Sanboda haka yadda za ku zama ubangidan kanku da kanku ya zama abin yayi.
A 2021, duniya ta buɗe sabbin hanyoyin sana'a, inda neman "ta yaya za a fara sabuwar sana'a" da kuma "ta yaya za a samu aikin yi" ya zama abin yayi.
A Amurka kaɗai, mutum fiye da miliyan huɗu ne suka rasa ayyukansu a watan Oktoba, a cewar wasu bayanai daga Sashen Kwadago.
Wasu mutanen sun ɗauki lokacin annobar a matsayin na yin karatun ta-nutsu ta yadda suka sauya sana'ar da ta fi ta da.
Google, mene ne NFT?
Wani maudu'in da ke da alaƙ da samun kuɗi shi ne NFT.
NFT - non-fungible tokens - hotuna ne ko kuma zane-zane da ake iya mallakarsu ta hanyar yi musu shaidar mallaka ta yadda za a iya saye ko sayar da su.
NFT ya kwana biyu, amma ba mu fara mayar da hankali kansa ba har sai da aka sayar da hoton bayanin farko da mamallakin Twitter Jack Dosey ya wallafa kan dala miliyan 2.9.
Da yake muna so mu gano sabbin damarmaki a intanet, maudu'in "ta yaya za a ƙirƙira" ya zama abin yayi shi ma.
Taurarin gidan sarauta
A watan Maris ne Yarima Harry na Birtaniya da matarsa Meghan Markle suka yi hirarsu ta farko da mai gabatarwa 'yar Amurka Oprah Winfrey bayan sun sauka daga muƙamansu na sarauta.
Wannan hirar ce ta zama hirar da aka fi yayi a shafin Google Trends a duniya baki ɗaya.
Ma'auratan sun bayyana yadda alaƙa ta lalace tsakaninsu da gidan Sarautar Birtaniya, suna masu zargin cewa an yi gulmar launin fatar ɗansu mai suna Archi.
Sai dai ba ita ce kaɗai aka yi yayi ba a ɓangaren fim na 2021.
Fim ɗin Koriya
Yayin da mafi yawanmu ke kulle a cikin gidaje, an samu isassehn lokacin kallon fina-finai a talabijin.
Squid Game, fim mai dogon zango da aka shirya a Koriya ta Kudu, shi ne fim ɗin da aka fi neman bayanai a kansa a duniya baki ɗaya.
Labari ne a kan wani rukunin mutane da ya zama dole su tsira daga wasu wasanni mai hatsarin gaske kafin su lashe kyautuka masu gwaɓi.
Fim ɗin ya ƙayatar da duniya, har ma ya zama wanda aka fi kallo a tarihin kamfanin Netflix.