'Fasinjoji 21 ciki har da jariri 'yan bindiga suka kona a wata motar fasinja a Sokoto, in ji 'yan sanda

yan bindiga

Asalin hoton, AFP

Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya ta ce akalla mutum 21 ne wasu 'yan bindiga suka kona a wata motar fasinja lokacin da suka yi musu kwanton-bauna.

Ta bayyana haka ne a wata hira da BBC Hausa ranar Laraba.

Sai dai wasu 'yan uwan fasinjojin sun ce mutanen da 'yan bindigar suka kona sun kai mutum 42.

Rahotannin sun ce fasinjojin sun fito ne daga karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar domin yin ƙaura zuwa wasu yankunan Najeriya, saboda ta'azzarar hare-haren 'yan bindiga a inda suke.

Wasu shaidu sun cewa BBC lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na safiyar ranar Litinin, sai dai ba a samu labari da wuri ba saboda matsalar sadarwa a yankin.

Tuni dai aka yi jana'ziar mamata, in ji shaidu.

'Abin da 'yan sanda suka ce'

Kakakin rundunar 'yan sandan jhar, Sanusi Abubakar, ya ce "mutum 19 ne suka mutu nan take yayin da mutum biyu suka mutu a asibiti."

Ya kara da cewa wasu daga cikin wadanda suka jikkata suna asibiti ana yi musu magani.

"Motar ɗauke da fasinjojin ta tashi daga Sabon Birni, ta yi tafiyar da bai fi kilomita shida ba zuwa kauyen Gidan Bawa inda wannan masifa ta afka mata," kamar yadda wadanda suka yi aikin ceton suka bayyana wa BBC.

Wani ganau ya gaya wa BBC cewa: "Lokacin da abin ya faru ina Sabon Birni aka kira ni aka shaida min. Daga cikin matafiyan ma har da wani ƙanin mahaifiyata da matarsa da ƴaƴansu huɗu.

"Cikin ƴaƴan Allah Ya yi wa biyu rasuwa. Lokacin da muka isa wajen da ya faru mun je mun iske mutane sun mutu, kuma a ƙalla mun ƙirga gawarwaki sun kai 25," in ji shi.

Ya ƙara da cewa akwai tsirarun mutane daga cikinsu da suka tsira.

Shi ma wani shaidan da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce "mutum 45 ne a cikin motar, amma bakwai ne suka tsira da rayukansu, su ma a yanzu haka suna cikin halin ha'ula'i.

"Babu maganar ma ka ga gawa a kammale, sai dai muka dinga haɗa ƙafafu da hannaye daban-daban aka yi musu jana'iza a tare."

Ya ce shi yana tsaye a tasha ma lokacin da motar ta tashi. "Ƴan Union ne ma na tasha suka gaya mana adadin mutanen da motar ta tashi da su," a cewarsa.

Yankin arewa maso yammacin Najeriya na ɗaya daga cikin yankunan da suka fi fama da matsalar tsaro a Najeriya, sai dai ba a cika samun labarin kona mutane ba.

Wasu labarai masu alaƙa