Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Garuruwan da aka fi yawan samun hatsarin jiragen ruwa a Najeriya
Hanyoyin ruwa na Najeriya na ƙara zama masu hatsari a ƴan shekarun nan inda ƙungiyoyi da dama a ƙasar suka yi ƙiyasin cewa tsakanin mutum 150 zuwa 350 ne suka mutu a 2020 kaɗai.
A watan Mayun 2021, mutum 30 ne suka mutu a yayin da wani jirgin ruwa ɗauke da mutum 100 ya ci karo da wani kututture a cikin ruwa a jihar Neja, lamarin da ya ja jirgin ya rabe gida biyu.
A watan Yulin 2020, wani jirgin ma ya nutse a jihar Benue da kusan mutum 30 a ciki, haka kuma mutum bakwai sun mutu a lokacin da jirgin ruwa ya nutse a daidai lokacin da ake ruwa mai ƙarfi a Legas, haka kuma wata ɗaya bayan haka an sake samun mutum takwas da suka mutu a wani hatsarin jirgin ruwan.
Hakazalika a ranar 26 ga watan Mayu, wani jirgin ruwa da aka yi wa lodi ɗauke da fasinjoji 150 zuwa 200 sun bar wani ƙauye da ke Lokon Minna a tsakiyar jihar Neja zuwa wata kasuwa a Warrah da ke Kebb.
Jirgin ya ɗauko fasinjoji a wasu wurare ba bisa ƙa'ida ba watakila domin kauce wa biyan haraji, sakamakon haka ne ya sa ba a san asalin adadin fasinjojin ba.
Jirgin dai tsoho ne wanda aka ƙera da katako kuma an ƙera shi ne domin ɗaukar fasinjoji 80 zuwa 150. Bugu da ƙari jirgin kuma ya ɗauko yashi daga wani wani wurin haƙar zinare.
An samu an ceto tsakanin fasinjoji 22 zuwa 26 jim kaɗan bayan faruwar lamarin. inda daga baya aka gano gaya 76. Ƴan sandan ruwa da masunta duk sun taimaka wajen ceto su.
Ba gano sauran fasinjojin ba inda aka kyautata cewa sun mutu.
Hatsarin jirgin ruwan Goronyo da Shagari
A watan Yunin 2021 ne mutum 13 suka mutu dukansu mata da kanana yara a cikin wani hadarin jirgin ruwa a jihar Sakkwato da ke shiyyar arewa maso yammacin Najeriya.
Lamarin dai ya faru ne a yankin karamar hukumar Shagari da ke kudancin jihar.
Kwale-kwalen ya kife ne lokacin da matafiyan ke da daf da kai wa inda za su domin hidimar aure.
Jirgin dai ya taso ne daga garin Ginga ɗauke da mutum 18, amma sai ya kife daf da ƙauyen Doruwa inda ya nufa; lamarin ya yi sanadin mutuwar mutum 13 yayin da biyar suka tsira.
'Yan mata bakwai sun rasu a hatsarin jirgin ruwa a Jigawa
A kwanakin baya ne wasu 'yan mata bakwai suka rasa rayukansu bayan da kwale-kwalen da suke tafiya a ciki ya kife ranar Alhamis da dare.
Lamarin ya faru ne lokacin da suke kokarin tsallaka wani kogi a kan hanyarsu ta dawowa daga taron Maulidi a garin Gasanya.
Bayanai sun ce jirgin na ɗauke da mutum 12 ne lokacin da ya kife a cikin kogin wanda ke tsakanin kananan hukumomin Auyo da Kafin Hausa, inda bakwai suka rasu, biyar suka tsallake rijiya da baya.
Mutanen dai na kan hanyarsu ne ta komawa garinsu na Gafasa da ke ƙaramar Hukumar Kafin Hausa daga Gasanya na karamar hukumar Auyo.
Malam Mikail Jibril, ɗaya ne daga cikin iyayen waɗanda suka rasu, kuma ya shaida wa BBC Hausa cewa shekarun 'yan matan bai wuce 11 ba zuwa 12.
Hatsarin jirgin ruwan Neja zuwa Kebbi
Aƙalla mutum 76 ne aka tabbatar da sun rasu a lokacin da wani jirgin ruwa ya dare gida biyu a lokacin da wani jirgin ruwa ya kife a hanyarsa ta zuwa Kebbi daga Neja.
Cikin fasinjojin har da mata da ƙananan yara da dama, kuma sun fito ne daga garin Lokon Minna mai yawan hada-hadar kasuwanci da ma'adinai a jihar Neja da ke yankin tsakiyar Najeriya.
A lokacin dca lamarin ya faru, sai da aka tura jiragen ruwa kimanin goma da kuma ayari-ayari na masu ninkaya domin laluben sauran mutanen da ba gani ba 165
Shaidu dai sun ce baya ga ɗauko ninkin adadin mutanen da ya kamata ya ɗauka, an kuma saka masa buhunan yashi da ake haƙowa daga mahaƙar zinare.
An dai gano gawarwaki 76 bayan an shafe kwanaki ana ta neman gawarwaki.
Hatsarin jirgin ruwan Kano
Hatsarin jirgin ruwa na baya-bayan nan shi ne wanda ya faru a Ƙaramar Hukumar Bagwai a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Waɗanda hatsarin ya rutsa da su akasarin su ƙananan yara ne kuma ƴan Islamiyya.
Rahotannin sun ce fiye da mutum 30 ne ake tunanin sun ɓata bayan hatsarin kwale-kwalen.
Bayanai sun nuna cewa mutanen sun taso ne daga ƙauyen Badau zuwa garin Bagwai domin yin maulidi amma kwale-kwalen ya nutse da su.
Rundunar 'yan sandan jihar ta ce kwale-kwalen yana dauke ne da mutum kusan 50.