Daliban Islamiyya da dama sun mutu a hatsarin kwale-kwale a jihar Kano

An ƙara samun gano gawarwaki tara a safiyar Laraba daga cikin mutanen da kwale-kwale ya kife da su a karamar hukumar Bagwai a jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya.

A ranar Talata ne hatsarin ya faru kuma yawancin fasinjojin yara ne ƙanana daliban Islamiyya.

Wakilin BBC a Kano ya ce jami'an ƴan sanda da ƴan kwana-kwana da masunta ne ke ci gaba da aikin ceton a ranar Laraba.

Amma kuma an dakatar da aikin ceton saboda iska da take kaɗa igiyar ruwan, sai dai za a ci gaba da yamma.

Rahotannin sun ce iye da mutum 30 ne ake tunanin sun ɓata bayan hatsarin kwale-kwalen.

Bayanai sun nuna cewa mutanen sun taso ne daga ƙauyen Badau zuwa garin Bagwai domin yin maulidi amma kwale-kwalen ya nutse da su.

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce kwale-kwalen yana dauke ne da mutum kusan 50.

A ranar Laraba ne kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida wa wakilinmu na Kano, Khalifa Shehu Dokaji, cewa "kwale-kwalen mai dauke da kusan mutum hamsin ya kife a kogin Bagwai.

"Ya zuwa yanzu mun gano gawar mutum 20, sai kuma mutum bakwai da aka ciro da ransu sanna ana ci gaba da neman wasu da dama da suka nutse."

Ganau sun shaida mana cewa jirgin ya nutse ne a kogin Bagwai sakamakon daukar mutane fiye da kima.

Hatsarin kwale-kwale ba wani sabon abu ba ne a Najeriya lamarin da yake matukar tayar da hankalin mutane saboda rashin daukar matakin daƙile shi