Sojin Najeriya sun ce sun kashe ɓarayin daji 128 da ƴan Boko Haram 140

Asalin hoton, HQ NIGERIAN ARMY/FACEBOOK
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe ɓarayin daji masu kai hare-hare da satar mutane 128 a arewa maso yammaci da kuma da ƴan Boko Haram 140 a arewa maso gabashin ƙasar.
Rundunar sojin ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta Bernard Onyeuko ya fitar inda ya bayyana irin nasarorin da ayyukan rundunonin sojin suka samu a sassan Najeriya da ke fama da matsalolin tsaro.
Rundunar ta ce alƙalumman sun shafi ayyukan rundunoninta na tsawon mako biyu daga ranar 11 ga Nuwamba zuwa 25 ga watan.
Sanarwar ta ce an yi wa sansanonin ƴan bindiga da ƴan Boko Haram ruwan wuta da kama wasu daga cikinsu.
Sai dai rundunar sojin ba ta bayyana yawan jami'anta da aka kashe ba a yaƙin da ƴan bindiga a arewa maso yammaci da kuma arewa maso gabashi da sauran sassan Najeriya da ke fama da matsalar tsaro.
Wannnan na zuwa ne bayan shugaba Muhammadu Buhari ya ba manyan hafsoshin tsaron ƙasar umarnin fatattakar ƴan bindigar da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja saboda ƙaruwar yawaitar hare-hare a sassan ƙasar
Ga nasarorin da rundunar sojin Najeriya ta ce ta samu:
RundunarHadin kai

Asalin hoton, NigerianArmy
Rundunar sojin Najeriyar ta ce, rundunar Hadin Ki ta kaddamr da hare-hare ta sama da kasa a maɓuyar mayaƙan Boko Haram da ISWAP a garin Baga na jihar Borno, mai iyaka da tafkin Chadi.
Ta ce an yi nasarar tarwatsa masu tada kayar bayan sakamakon samun bayanan sirrin cewa wasu daga cikin mayakan kungiyoyin biyu sun isa tafkin Chadi a kwale-kwale.
Rundunar ta ce a farmakin da ta kai yankin Askira Uba, an kashe sama da mayaƙan Boko Haram 50, an kuma yi nasarar kwace wasu daga cikin makamansu, ciki har da ma'ajiyar albarusai, da manyan motocin yaƙi da sauran makamai.
Har wa yau, sojoji da ke garin Baga, sun yi nasarar kama wani kasurgumin dan ta'adda mai suna Haladu Saleh, wanda jami'an tsaro ke nema ruwa a jallo tun a shekarar 2018.
Sannan a wuraren binciken ababen hawa a Bukarti da Yusufari da kuma Maima Hari a hanyar Biu zuwa Damboa, an kama wani da ake zargi da kai wa 'yan ta'adda kayayyaki bayan samun bayanan sirri da ke cewa 'yan ta'addan na fakewa a kauyen Karawa.
An yi nasarar cafke Mista Ezekiel Karson da Galadima Bako wadanda ke kai wa 'yan ta'addan muggan kwayoyi ciki har da tabar Wiwi.
A lokacin wannna aiki an kashe sama da 'yan ta'adda 90, da cafke wasu 50.
Rundunar Hadarin Daji

Asalin hoton, NigerianArmy
Sanarwar ta ce rundunar Hadarin Daji ta kaddamar da hare-hare ta kasa da sama a jihohin Nasarawa da Katsina, inda suka kama masu kai wa 'yan ta'addan kayan bukatun yau da kullum da suka hada da Alhaji Lawal Auwalu, da Ibrahim Tayo da Alhaji Dahiru Abubakar.
Sojojin kuma a farmakin da suka kai Batsari ta jihar Katsina an kama masu kai wa ɓarayin makamai, an kuma yi musuyar wuta tsakanin jami'an tsaro da 'yan bindigar.
Rundunar sojin ta ce ta nasarar lalata sansanonisu ciki har da maɓuyar wani kusurgumin ɗan fashi mai suna Bello Guda Turji da abokin aikinsa Bello Buza da ke ayyukansu a jihohin Sokoto da Zamfara.
Sojojin na Najeriya sun ce sun kama 'yan ta'adda 12, da barayin daji 118, an kubutar da mutum biyar da aka yi garkuwa da su, an kama makamai 26, da miliyoyin albarusai.
Sannan rundunar ta jagoranci taron tsaro da shugabannin yankunan, da shugabannin matasa da masu ruwa da tsaki kan matsalar tsaro da arewacin Najeriya ke fama da shi.
An kuma gudanar da irin wannan taron a shalkwatar tsaro da ke Abuja babban birnin kasar.
Rundunar Safe Heaven
A cewar sanarwar rundunar Safe Heaven ta kai irin nata farmaki kan masu tada kayar baya da ke garuruwan, Bassa da Bokkos da ke kudancin birnin Jos da kudancin Mangu, da Riyom, da Barki Ladi, da Shendam duka a jihar Filato.
Sun yi nasarar sasanta rikici tsakanin wasu makiyaya da manoma da iyalansu suke ta zubda jini tsakaninsu.
Sojojin sun ce sun kuma yi nasarar kubutar da wasu da 'yan bindiga suka sace da kwato makamai da albarusai.

Sojojin Najeriyar sun kuma ce sun yi nasarar dakile wasu daga cikin ayyukan da ba ta gari ke aikatawa a kudancin kasar, sun kuma dakile ayyukan kungiyar IPOB da ke fafutikar ɓallewa daga Najeriya da kafa ƙasar Biafra.
Sojoji sun ce kama wasu daga cikin mayakan IPOB tare da mika su ga hukumomin da suka dace domin fuskantar sharia.
Sai dai duk da koƙarin da sojojin suka ce sun yi amma hare-hare na ci gaba da ƙaruwa musamman a arewa maso yammacin Najeriya.
Wani rahoto da Kamfanin Beacon Consulting da ke nazari kan matsalar tsaro a Najeriya ya fitar, binciken ya ce an kashe mutum 636 a watan Oktoba kaɗai a sassan Najeriya.











