Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An far wa mata da ke gangamin neman 'yancinsu a Turkiyya da Mexico
'Yan sandan kwantar da tarzoma a Turkiyya da Mexico sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye a kan masu zanga-zangar neman kawo karshen cin zarafi da muzguna wa mata da ake yi.
Dubban masu zanga-zanga ne suka yi tattaki a ranar duniya ta kawo karshen hare-haren da sauran abubuwa na gallaza wa da ake yi wa mata, saboda jinsinsu.
Daruruwan mata ne suka yi tattaki a babban birnin Turkiyya, Santambul, a gaban dimbin jami'an tsaro da aka girke a tsakiyar birnin.
Sai dai girma-girma macin ke gudana, amma isar jerin gwanon dandlin Taksim ke da wuya sai wasu daga cikin matan suka yi kokarin keta shingen tsaron da aka yi a wurin, abin da jami'an tsaron suka ga ba za su lamunta da shi ba, inda daga nan sai suka fara harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar, abin da ya tayar da hanakalin wasunsu.
Matan dai na nuna ɓacin ransu ne da matakin gwamnatin Turkiyya na janyewa daga yarjejeniyar da aka cimma ta duniya, wadda aka sanya wa hannu a birnin na Santambul shekara goma da ta wuce, wadda ta tanadi kokarin rage cin zarafin da ake yi wa mata.
Turkiyya ce kasa ta farko da ta sanya hannu a yarjejeniyar ita ce kuma ta farko da ta janye daga ciki a watan Yuni.
Wasu daga cikin 'yan jam'iyya mi mulki ta Shugaba Recep Tayyib Erdogan suna ganin cewa yarjejeniyar ba ta dace da dokokin Musulunci da kasar ke bi ba.
Shugaba Erdogan ya ce kasar za ta yi amfani da dokokinta wajen kare hakkin mata, amma ba wasu dokoki na daban ba.
Kungiyoyi da yawa a ciki da wajen kasar ta Turkiyya, da ke nuni da irin karuwar da ake samu ta muzguna wa mata sun yi kakkausar suka kan ficewar kasar, tare da neman gwamnati da ta sauka.
Wasu kungiyoyin kare hakki sun ce an kashe mata akalla 345 a Turkiyya a shekarar nan.
Can a babban birnin kasar Mexico wato Mexico City ma an samu yamutsi tsakanin 'yan sanda da mata masu zanga-zanga inda jami'an suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye, domin tarwatsa matan 'yan kadan da suka hallara a lokacin da suka yi kokarin kama garkuwar jami'an, wadanda suka yi musu shinge.
Matan dai na neman ganin an kawo karshen ta'adar kashe mata da ake yi ne saboda kawai su mata ne.
An yi kiyasin cewa a kullum ana kashe mata da 'yan mata akalla goma a kasar ta Latin Amurka, kamar yadda wani bincike na Amnesty International ya nuna.
Daga cikin masu zanga-zangar da suka rufe kansu sun rika jefa wa 'yan sanda kwalabe da duwatsu, wuta, kamar ydda rahotanni suka bayyana
Mutane goma sha bakwai ne wadanda suka hada da 'yan sanda mata goma suka ji rauni a yayin dauki-ba-dadin. In ji 'yan sanda.
An dai yi irin wannan gangami na ranar duniya ta neman 'yancin mata a birnen Barcelona da Paris da London.