Haile Gebrselassie da Feyisa Lilesa na Ethiopia sun shirya zuwa fagen daga

Haile Gebrselassie

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Haile Gebrselassie

Shahararrun 'yan ƙasar Habasha da suka yi nasara a gasar Olympics a shekarun baya Haile Gebrselassie da Feyisa Lilesa sun bayyana cewa a shirye suke su je fagen daga domin yaƙar ƴan tawayen yankin Tigray na Habasha.

Wannan sanarwar tasu na zuwa ne bayan Firaiministan ƙasar Abiy Ahmed ya bayyana cewa zai tafi fagen daga domin jagorantar yaƙin.

Ƴan tawayen na Tigray sun ce suna hanyarsu ta shiga Addis Ababa babban birnin ƙasar.

Jamus da Faransa sun zama ƙasashe na baya-bayan nan da suka ba yan ƙasashensu shawara su bar Habasha a daidai lokacin da yaƙi ke ƙara ruruwa a ƙasar.

A ranar Talata, manzo na musamman da Amurka ta tura a yankin, Jeffrey Feltman, ya bayyana cewa ana yi wa shirye-shiryen difilomasiyya na musamman domin kawo ƙarshen yaƙin zagon ƙasa .

A farkon makon nan ne ƴan tawayen suka bayyana cewa sun ƙwace iko da Shewa Robit, wani gari mai nisan kusan kilomita 225 daga Addis Ababa. Sai dai babu wata hujja gamsasshiyya da ta tabbatar da wannan iƙirari.

Ministan watsa labarai na ƙasar Legese Tulu ya bayyana cewa sojojin ƙasar "sun samu nasarori" tun bayan da Mista Abiy ya bayyana aniyarsa ta zuwa fagen daga, inda ya ce ana daf da samun nasara.

Ganin cewa Mista Abiy zai kama hanyarsa ta zuwa wajen yaƙi, mataimakinsa Demeke Mekonnen Hasse ya karɓi ragamar jagorancin ƙasar, kamar yadda aka ruwaito mai magana da yawunsa yana cewa.

Sanarwar da Mista Abiy ya yi ta ƙara ƙwarin gwiwa wajen ɗaukar aikin soji a ƙasar, inda ɗaruruwan mutane ne suke halartar aikin ɗaukar inda suke rera waƙoƙin kishin ƙasa a Addis Ababa a ranar Laraba.

An ruwaito Gebrselassie mai shekara 48 na cewa "A shirye nake na yi duk wani abu da ake buƙatar na yi, ciki har da zuwa yaƙi," in ji shi.

Ana kallon Gebrselassie a matsayin wani gwarzo a Habasha, kuma ana kallon kalaman da ya yi a matsayin wani yunƙuri na jawo mutane su shiga yaƙin.

A shekaru 25 da ya shafe yana wasanni, ya samu kyautar zinare har sau biyu a gasar Olympics, ya yi nasara a duniya sau takwas kuma ya kafa tarihi sau 27 a duniya. A 2015 ne ya sanar da cewa zai yi ritaya.

A lokacin da yake bayyana goyon bayansa ga wannan yaƙi, an ruwaito Feyisa Lilesa mai shekara 31 yana cewa a shirye yake ya tafi fagen daga domin ceto ƙasarsa ta kaka da kakanni.

Ɗan wasan ya samu kyautar azurfa a gasar Olympics da aka yi a Rio a 2016.

..

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Feyisa Lilesa

Ya shahara bayan ya ɗaga hannayensa sama ya gicceyesu kamar an saka masa ankwa domin jawo hankalin duniya a lokacin da ake zanga-zangar neman kawo sauyin siyasa a Habasha.

A lokacin da lamarin ya faru, Jam'iyyar Tigray People's Liberation Party wato TPLF ce ke jagorantar ƙasar. Bayan zanga-zangar, Mista Abiy ya karɓi jagorancin ƙasar inda TPLF ta rasa iko da ƙasar bayan ta shafe shekara 27 tana jagoranci.

Daga baya TPLF ɗin ta koma yankin da ta fi ƙarfi wato Tigray inda daga nan ne ta ƙaddamar da tawaye a Nuwambar da ta gabata bayan irin sabbin sauye-sauye da Mista Abiy ya kai ƙasar.

Yaƙin da ake yi ya jawo matsaloli musamman na ƙarancin abinci inda dubban mutane ne suka mutu, lamarin da ya yi sanadin miliyoyin mutane suka bar gidajensu dubbai kuma suka faɗa cikin halin yunwa inda ƙungiyoyin agaji ke ci gaba da ƙoƙarin kutsawa cikin yankunan da lamarin ya shafa.

Ƙungiyar haɗin kan Afrika na jagorantar wani shiri na sasantawa domin kawo ƙarshen wannan rikici amma babu wani ɓangare da ya mayar da hankali wajen tattaunawa.

Ƴan TPLF na ƙara matsawa gaba domin shiga Addis Ababa kan babbar hanyar ƙasar inda baya suka ce sun ƙwace iko da Kemise.

Sharhi daga Andrew Harding

Labarin da aka samu cewa akwai wasu shahararrun ƴan wasa da suka kama hanyarsu ta tafiya fagen daga wani lamari ne da ya ja hankulan mutane a Addis Ababa.

A lokacin da yaƙin ya ƙara ƙamari, akwai ƴan Habasha da dama da ke yawo kan tituna suna ɗaga tutar ƙasar da hoton firaiminista, inda suke ƙoƙarin bayar da gudunmawarsu wajen neman goyon bayan jama'a ga sojojin ƙasar da suka yi ta samun cikas a yaƙin da suke yi a ƴan watannin nan, duk da cewa har yanzu akwai tantama kan batun irin alƙaluman da aka fitar na waɗanda suka jikkata a fagen daga.

A bayyane take cewa mutane da dama na kallon barazanar da sojojin ke yi wanda TPLF suka jawo da ƙawayensu a matsayin wata matsala ga Habasha.

Bayan haka kuma akwai wani baƙin jini ga ita kanta TPLF ɗin, wanda ya samo asali ne bayan ta shafe shekaru tana jagorancin ƙasar. Amma akwai wasu abubuwan ma da suka fi hakan.

Firaiministan ƙasar ya nuna wa duniya ƙasarsa a matsayin wadda ta shiga wani hali, ba wai batun rikicin Tigray ba kaɗai, amma zargin da yake yi na wasu ƙasashen duniya na rage ƙarfin Habasha ta hanyar hukuntata domin ta ƙi bai wa Turawan mulkin mallaka kai bori ya hau.

Ana kallon kafafen yaɗa labarai na ƙasashen yamma a matsayin masu goyon bayan makirci - wanda ake ganin ya karɓu a ƙasar inda ake ƙoƙarin bayani kan yadda ƴan tawayen ƙasar suka ƙara ƙarfi.

Map of Ethiopia