Ethiopia: Hotunan karya da ake yadawa kan yunwa a Amhara

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Peter Mwai
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reality Check
Bazuwar da rikicin Tigray da ke yankin arewacin Habasha ya yi zuwa yankin Amhara da ke makwabtaka ya raba dubban mutane da mahallansu, tare da jefa daruruwa cikin matsalar karancin abinci.
Hotunan da ake yadawa a kafafen sada zumunta na nuna mata da yara kanana da ke fama da tamowa.
Amma daga baya mun gano wasu hotunan ma ba a kasar aka dauke su ba sun faru ne da dadewa a wani wuri na daban - daga Somaliya da Tigray da kuma lokacin da aka yi fama da fari a Habasha a 1984.
Yaya matsalar karancin abinci a yankin Amhara?
Gwamnatin Habasha ta ce yawan wadanda suka rasha muhallansu a wannan rikicin ya kai 500,000, wadanda kuma suke bukatar abinci sun haura miliyan guda.
Wani taimakon abincin da ake kai wa na zuwa inda ake bukata, amma gwamnati ta ce 'yan adawa na kawo koma baya wajen shigar da kayan agaji yankin da abin ya fi shafa na lardin Wollo da ke arewacin Amhara.
"Mayakan TPLF na hana masu kai kayan agaji kai wa ga fararen hula masu matukar bukata, " in ji Billene Seyoum, kakakin Firaiministan kasar.

Asalin hoton, Getty Images
TPFL ta zargi gwamnati kan rikicin da ke faruwa, ta yanke huldar sadarwa a yankuna da yawa da kuma wutar lantarki.
Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya ce yayin da dubbai ke bukatar abinci a wasu yankunan Amhara, "a wannan matakin ba mu da shaidar cewa ana fama da matsanaciyar yunwa a arewacin Wollo".
"Har yanzu ana ci gaba da fama da wannan matsala kuma wasu yankunan masu yawa ana ci gaba da yaki a yankunan, matsalar karancin abinci na kara ta'azzara a yankin," in ji WFP.


Hotunan karya
Mun gano wasu hotuna masu yawa na karya da ake amfani da su wajen janyo hankali masu aikin ba da agaji a yankin Amhara.
An ta yada wasu hotuna a Twitter kan yadda yanayi yake a yankin, amma daga baya mun gano hotunan karya ne.
Mun bibiyi hotunan zuwa 2011, inda aka yi amfani da su a wani labarin farin da aka samu a Somaliya da kuma wani yanki na Habasha (Ogaden).


Wasu daga cikin hotunan da muka yi amfani da su a kasa suma na karya ne.
Hoton da ke ta bangaren hagu an dauke shi ne a Somaliya, a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke kudancin Mogadishu babban birnin kasar a 2011.
Wannan da yaron nan yake a kwance a kasa an dauke shi ne a watan Mayu a wannan shekarar a wani asibiti da ke Makele babban birnin Tigray.
Amma hoto na uku bai nuna cewa a Amhara aka dauki hoton ba. An dauke shi ne a cikin wani bidiyon yankin a farkon wannan wata, kuma ana yada cewa na wasu mata ne da ke gudun hijira a yankin arewacin Wollo.
An kuma kara aika sakon sama sama da 10,000.

Hoton da kuke gani na kasa da aka makala a jikin wannan Twitter an nuna na mata ne da wasu kananan yara da suka fito daga yankin Amhara.
Bayan haka kuma mun bibiyi wanda ya fara amfani da wannan hoton a watan Mayu a yankin Tigray. Wasu mutanen da suka gujewa yankin na neman mafaka a wata makaranta a Makele.


A karshe wannan hoton shima an yada shi a Twitter kuma mun gano haka, wanda yake nuna matsalar karancin abincin da ake fama da shi a yankin Amhara, an yi amfani da shi da launin fari da baki kuma an dauke shi ne a 1984, lokacin da dubban daruruwan mutane da suka mutu.












