Gobara ta hallaka yara 'yan makaranta fiye da 20 a Maradi ta Nijar

Bayanan bidiyo, Bidiyon jana'izar daliban makarantar firamare ta Maradi

An yi jana'izar yara 26 da suka rasu sakamakon gobara a wata makarantar nazare da firamare da ke Maradi a yankin kudancin Nijar.

Lamarin ya faru ne ranar Litinin 8 ga watan Nuwamban 2021, kuma yaran da suka rasu 'yan tsakanin shekara uku ne zuwa takwas.

Har yanzu babu cikakkun bayanai kan abin da ya haddasa gobarar wadda ta soma daga rufin azuzuwan da aka gina da katako.

Akwai kuma dalibai da dama da suka ƙone, yanzu haka na samun kulawa a asibiti.

Tun a ranar da abin ya faru gwamnati ta rufe makarantun jihar Maradin tare da ƙaddamar da zaman makoki na tsawon kwanaki uku.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake ta ƙoƙarin zakulo mutanen da ake zargin sun maƙale a wani waje da ake hakar gwal a yankin jihar ta Maradi.

An sha samun irin wannan iftila'in a Nijar a wannan shekarar- ciki har da wanda ya yi ajalin dalibai 20 a birnin Yamai cikin watan Afrilu.

Babban daraktan kula da ilimi a jihar Katsinar Maradi ne ya bayar da sanarwar rufe makarantun, da kuma zaman makokin na tsawon kwanaki uku, daga gobe Talata zuwa Alhamis, a iya fadin garin Maradi, babban birnin jihar.

Gobarar ta tashi a safiyar Litinin a makarantar renon yara da firamare ta AFN ta kungiyar mata a garin a unguwar Sabon Gari, kusa da babban filin kwallo na garin Maradin.

jana'izar yara a Maradi
jana'izar yara a Maradi
jana'izar yara a Maradi

Saminou Salisou Rijiyar Lemo, wani dan jarida mazaunin garin na Maradi, ya yi karin bayani kan aukuwar wannan al'amari inda ya ce abin ya yi muni sosai.

"Iyaye maza da mata sun cika asibitin suna ta koke-koke suna cikin mawuyacin hali. Wasu iyayen ma da suka je asibitin ba su ga ƴaƴan nasu ba, don da yawa ba a ma gane fuskokinsu saboda ƙonewar da suka yi.

"An samu wutar ta mutu tun misalin ƙarfe ɗaya na rana, to amma ana ta ɗibar gawarwakin mutane ana tafiya da su asibiti."

"Zuwa yanzu dai likita ya ce akwai kusan mutum 22 da suka mutu, sannan da wasu 17 suna karɓar magani," in ji shi.

Saminou Salisou ya ce gwamnan jihar ya je wajen kuma ya yi wa iyayen yara jawabin kwantar da hankali tare da yi musu alkawarin yin duk abin da ya dace don ceto waɗanda suka jikkata.

Sai dai ya ce har yanzu ba a san abin da ya haddasa gobarar ba. "Kusan mutum 250 ne a makarantar kuma ajujuwan na zana ne.," in ji ɗan jaridar.

Wannan gobara ta auka ne yayin da ake ƙoƙari ceton mutanen da riftawar wani rami ta rutaa da su a wani waje da ake haƙar gwal a garin Dan Isa na yankin jihar Katsinar Maradin, inda rahotanni ke cewa ya zuwa yanzu mutum fiye da 30 sun rasa rayukansu.

Bazoum

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Hakan ya auku ne yayin da ake ta ƙoƙarin zakulo mutanen da ake zargin sun maƙale a wani waje da ake hakar gwal a yankin jihar ta Maradi