Nijar ta ayyana zaman makoki na kwana biyu bayan kashe kusan mutum 70

Asalin hoton, AFP VIA GETTY IMAGES
Jamhuriyyar Nijar ta ayyana zaman makoki na kwanaki biyu daga yau Juma'a bayan da wasu da ake zargi masu ikirarin jihadi ne sun kashe kimanin mutum 70.
Harin ya faru ne a kudu maso yammacin ƙasar ta kan iyakar Nijar ɗin da Mali.
Cikin waɗanda harin ya rutsa da su har da wani magajin gari da kuma shugaban wata rundunar sa kai, kamar yadda gwamnatin ƙasar ta bayyana. A yanzu dai ana ci gaba da neman waɗanda suka tsira.
Babu wata ƙungiya da ta fito ta ɗauki nauyin kai harin. Waɗanda suka kai harin sun tsere ta iyakar ƙasar da Mali inda rahotanni suka ce sun ɗauke gawargwakin ƴan uwansu da aka kashe.
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Jamhuriyyar Nijar ɗin ta kuma ce an yi wa wani ayari ƙarƙashin jagorancin Magajin Garin Banibangou kwantar ɓauna a wani ƙauye da ke da nisan kilomita 55 daga wurin da lamarin ya faru a Yammacin Tillaberi.
Gwamnatin ƙasar dai ta ce wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi kwantan ɓaunar.
Ƴan bindiga dai da ke da alaƙa da ƙungiyar IS na cin karensu ba babbaka a yankin.
Jamhuriyyar Nijar na fuskanatar hare-haren masu i kirarin jihadi a iyakokinta da Mali da Burkina Faso da Najeriya.
Sama da mutum 500 ne aka kashe sakamakon irin waɗannan rikice-rikicen a kudu maso yammacin ƙasar a bana.











