Ƴan Nijar sun kai ƙarar Faransa kan zargin kisan ƙare dangi

Bayanan sautiƳan Nijar sun kai ƙarar Faransa kan zargin kisan ƙare dangi

Latsa hoton sama domin sauraren shirin

A ranar ne Talata da ta gabata wani mai gabatar da kara na musamman na Majalisar Dinkin Duniya, ya shigar da kara a majalisar a birnin Geneva, a madadin wasu al’ummomi a Jamhuriyar Nijar, kan kisan ƙare dangin da ake zargin wasu Faransawa da aikatawa a kasar a lokacin mulkin mallaka.

Tarihi ya nuna cewa Voulet et Chanoine sun hallaka dubun dubatar jama’a a Nijar ɗin, yayin da suke ƙoƙarin mallakar kasar da sunan Faransa.

Shigar da ƙarar ta biyo bayan film din ‘African Apocalypse’, wanda wani ɗan Birtaniya Rob Lemkin ya shirya kan aika-aikar, wanda BBC ta watsa.

A shirin Gane Mani Hanya, Aichatou Moussa ta tattauna da Malam Husseini Tahirou Amadou tsohon malamin tarihi kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka shigar da karar.

Ya fara ne da yin bayani kan kashe-kashen da aka yi a Nijar din