Liverpool na son Phillips, PSG na neman Raphinha

..

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool ta bi sahun Manchester United wajen neman ɗan wasan tsakiyar Leeds da Ingila Kalvin Phillips mai shekara 25 a cinikin fam miliyan 60. (Star)

Ita ma Paris St-Germain ta bi sahu wajen ƙoƙarin sayen ɗan wasan Leeds Raphinha mai shekara 24 bayan ta samu bayanai masu armashi kan ɗan wasan daga takwaransa na Brazil Neymar. (Teamtalk)

Liverpool na daga cikin ƙungiyoyin da suka nuna sha'awar sayen ɗan wasan tsakiyan Ingila Jude Bellingham mai shekara 18 daga Borussia Dortmund. (Sport1, via Sun)

Marc Overmars zai bar Ajax domin zama daraktan ƙwallon ƙafa a Newcastle a tsakanin Janairu ko Fabrairu mai zuwa. (De Telegraaf via Voetbal Primeur - in Dutch)

Za a tilasta wa Manchester United biyan Ole Gunnar Solskjaer fam miliyan 7.5 a matsayin diyya idan suka sallame shi a yanzu. (Sun)

'Yan wasan Manchester United na bayan Solskjaer a lokacin wani bincike a dakin sauya kayan 'yan kwallo. (Times - subscription required)Dan wasan tawagar Portugal, Cristiano Ronaldo, mai shekara 36 ya yi kokarin jan ragamar karfafa gwiwa a dakin sauya kayan 'yan wasan Manchester United da su mara wa kocin baya.

..

Asalin hoton, Getty Images

Newcastle ta sa ido kan ɗan wasan gaban Bayer Leverkusen mai shekara 18 Florian Wirtz a yayin da ɗan wasan na Jamus ya taka leda a wasan da suka buga da Cologne a ranar Lahadi. (Bild - in German)

Borussia Dortmund na tattaunawa da Chelsea kan makomar ɗan wasan gaban Jamus Timo Werner mai shekara 25 da kuma ɗan wasan Ingila Callum Hudson-Odoi mai shekara 20 da kuma ɗan wasan Amurka Christian Pulisic mai shekara 23. (Teamtalk)

Michael Edward na shirin barin aikinsa a matsayin daraktan wasannin Liverpool a ƙarshen kaka kuma ɗan wasan mai shekara 41 ba shi da wani buri bayan hakan. (Football Insider)

Barcelona ta yi tuntuɓa game da ɗan wasan bayan Monaco da Brazil Henrique mai shekara 24. (AS - in Spanish)