Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaben shugabancin jam'iyyar APC ya bar baya da kura a Kano
A Najeriya zaben shugabannin jam'iyyar APC mai mulkin kasar, wanda aka gudanar a matakin jihohi ya bar baya da kura, inda a wasu jihohi aka samu bangarorori daban-daban da ke ikirarin cewa su ne halatattun wadanda ya kamata su gudanar da wadannan zabuka.
Jihar kano na daga cikin jihojin da aka gudanar da zaben a wurare biyu daban daban inda aka ja layi tsakanin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da kuma tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahin Shekarau.
A ranar asabar ne dai uwar jam'iyyar APC ta amince a gudanar da zaben shugabannin jam'iyyar a matakin jiha.
Tun safiyar Asabar ne masu zaben shugabanin jam'iyyar APC wato delegate a matakin jiha a Kano suka yiwa filin wasa na Sani Abaca tsinke inda aka fara tantance masu zaben da suka zo daga kananan hukumomi 44 dake jihar a harabar filin Wasa na Sani Abaca.
Kuma Barista Auwalu Abdullahi shugaban kwamitin gudanar da zaben shuwagabanin jam'iyyar APC a matakin jihar da uwar jam'iyyar APC a Najeriya ta aika Kano, ya bayyana cewa Abdullahi Abbas ne ya yi nasara da kuri'u 3,122 hakan ya bashi damar zama sabon shugaban jam'iyyar APC na jihar.
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje y ace sakamakon zaben babbar nasara ce ga jihar Kano, kuma sun san cewa anan ne uwar jam'iyya ta aiko wakilai har guda Bakwai wadanda akan idon su komai ya gudana kuma sun tabbatar an yi zaben nan cikin gaskiya da adalci.
Kuma babu wasu jami'ai da aka tura wasu waje zabenb da aka yi na sus hi ne halattace, amma ga wadanda suke hamayya babu wani dan dimukradiyya da zai so irin hamayyar mara asali ba.
Ganduje ya kara da cewa tun da duka 'yan uwa ne kuma wasu shugabanni ne sai a zauna da su domin a san matsalarsu a kuma warwareta.
To sai dai tsagin dake rikici da bangaren gwamnan Kano karkashin jagorancin sanata Ibrahim Shekarau suma sun gudanar da nasu zaben a janguza a yankin karamar hukumar Tofa dake jihar, inda suka zabi Alhaji Ahmad Haruna Zago a matsayin na su shugaban jam'iyyar.
Da farko dai sun shirya gudanar da zaben nasu ne a cibiyar koyar da Matasa sana'o'i ta Sani Abacha dake kan hanyar zuwa Madobi, amma sai dai tun kafin su isa wannan waje jami'an 'yan Sanda na Anti Daba suka yiwa wajen tsinke.
Daga bisani suka yi zaben a Janguza dake yankin karamar hukumar Tofa kuma suka bayyana Ahmad Haruna Zango a matsayin zababen shugaban jam'iyyar APC a Kano.
Honarabul Tijjani Abdulkadir Jobe daya ne daga jagororin da suka shirya nasu zaben karakshin jagorancin tsohon gwamnan Kano Sanata. Ibrahim Shekarau, sun ce bangrensu shine zaben da uwar jam'iyyarsu ta APC ta yarda dashi.
''Akwai jami'an gabatar da zabe sun je daya wurin sun kuma je inda Mukai zabe idan ba mu saurari jam'iyya ba ai hakan ba za amince ba. Don haka zaben da muka yi shi ne halattace, mu ne akan tsari, sub a shugabanni ba ne, ba su da wata dama da za su ce sun gudanar da zabe,'' inji shi.
Ba wai iya jihar Kano kadai ake fama da rikicin zaben shugabanci ba a jihohin Najeriya, a jihohi irinsu Oya an sakamkon zargin yunkurin magudi a zaben shugabnin jihar uwar Jam'iyyar ta yiwa kwamitin da ta aike da ya shirya zabe a can, ya koma babban ofishin ta dake Abuja domin daukar mataki na gaba.
Haka zalika wasu rahotannin sunce an yi harbe-harbe a wurin taron jam'iyyar APC a Jihar Ogun da ke kudancin ƙasar, lokacin da ake tsaka da zaɓen shugabannin jam'iyyar da wani ɓangare ya shirya ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamanan jihar Ibikunle Amosun a fadar basaraken Abeokuta, Alake na Abeokuta.
Duk da cewa babu tabbacin abin da ya haddasa harbe-harben, magoya bayan jam'iyyar sun shiga ruɗani tare da neman mafaka lokacin da wurin ya hautsine, sai dai rahotannin sun ce an ci gaba da ayyukan zaɓen bayan jami'an tsaro sun shawo kan lamarin.
Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ita ma babbar jam'iyyar adawa ta PDP ke gudanar da tarukan zaɓen a wasu jihohin ƙasar duk dai a ranar Asabar.