Hotunan ziyarar Shugaba Buhari a jihar Imo

A ranar Alhamis ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Imo da ke kudu maso gabashin kasar.

Shugaban ya samu gagarumar tarba daga 'yan jihar, duk da kiran da kungiyar 'yan a-aware ta IPOB ta yi kan mutane su zauna a gidajensu.

Buhari ya kaddamar da jerin ayyukan da gwamnatinsa da ma gwamnatin jihar suka yi a jihar.

Ga wasu hotunan ziyarar shugaban kasar:

A cikin ayyukan da Shugaba Buhari ya kaddamar har da tashar karkashin kasa mai suna Chukwuka Nwoha.

Haka kuma ya kaddamar da hanyar Naze zuwa Nekede zuwa Ihiagwa.

Kazalika ya kaddamar da titin Egbeada da ke Amakohia

Shugaba Buhari ya kuma bude sabon dakin taron majalisar zartarwar jihar da ke Gidan Gwamnatin jihar mai suna Douglas House

Shugaba Buhari ya gana da wasu shugabannin Kudu maso Gabas.

Ziyarar tasa tana da muhimmanci ganin cewa gwamnan jihar Imo Hope Uzodimma, wanda dan jam'iyyar APC ne, yana daga cikin shugabannin yankin da ke goyon bayan manufofin shugaban kasar.

Sai dai an rufe wasu kasuwannin da ke kusa da wuraren da shugaban ya kai ziyara domin tabbatar da tsaro.