Khalid Sheikh Mohammed: "Yadda mutumin da ya kitsa harin 9/11 ya kufce daga hannuna"

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Gordon Corera da Steve Swann
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilan BBC
Mutumin da ake zargi da shirya kutunguilar tashi da kuma yin garkuwa da jiragen fasinjojin na shekaru 20 da suka gabata har ta kai ga sun yi karo da katafariyar hasumiyar cibiyar kasuwanci ta birnin New York a Amurka ana tsare da shi yana jiran shari'a.
Amma shin za a iya daƙile aniyar tasa ne tun kafin ya kai ga aiwatar da ita a wancan lokaci?
"Mutumina ne"
Frank Pellegrino yana zaune a wani dakin otal a Malaysia lokacin da ya ga hotunan talabijin na jiragen da suka yi karo da juna yayin lamarin.
Abu na farko da ya zo masa a rai shine "Na shiga uku, daga gani wannan aikin Khalid Sheikh Khalid ne".
Manufa da burin da ya sa aka yi hakan sun yi dai-dai da juna, kuma Pellegrino shi ne wanda ya fi dacewa ace ya san komai tattare da wannan batu.
Tsohon jami'i na musamman na hukumar tsaro ta FBI ya bibiyi Mohammed tsawon kusan shekaru talatin, amma duk da haka wanda ake zargi da kitsa harin na 9/11 bai fuskanci shari'a ba.
Lauyan Mohammed ya shaida wa BBC cewa za a iya kwashe shekaru 20 kafin a kammala shari'ar.

Asalin hoton, Getty Images
Ana ganin cewa Osama Bin Laden ne ya kitsa harin na 911 lokacin yana shugaban ƙungiyar al-Qaeda, amma a kashin gasiya Khalid ne mafi kusanci da harin, domin shi ne mutumin da ya bijiro da dabarar ya kuma gabatarwa Osama Bin Laden a cewar hukumar binciken harin na 911, kuma Frank Pellegrino na kan gaba wajen gano hakan.
An haife shi a Kuwait, ya yi karatu a Amurka kafin yaƙi a Afghanistan a shekarun 1980. Shekaru kafin harin 9/11.
A lokacin da ake binciken ne sunan Khalid ya fara bayyana ga mahukuntan Amurka saboda an gano cewa ya aika wa daya daga cikin wadanda suka tsara harin kudi ta banki.
Wakilin FBI ya fahimci girman burin Mohammed a 1995 lokacin da aka alakanta shi da wani shiri na tayar da jiragen sama da yawa na duniya a kan tekun Pacific.
A tsakiyar shekarun 1990 ne fatan Pellegrino na kama Khalid ya kusa cika, inda ya bi shi har zuwa Qatar.
Shi da wata tawaga sun tafi Oman daga inda suka shirya tsallakawa zuwa Qatar don kama Mohammed. Jirgin ya shirya don dawo da wanda ake zargi. Amma akwai turjiya daga jami'an diflomasiyyar Amurka a kasar.
Pellegrino ya je Qatar ya shaida wa jakadan Amurka a kasar da sauran jami'an ofishin jakadancin cewa yana tuhumar Mohammed kan shirin da ya shafi harin harin na 911. Amma ya ce da alama su a can suna takatsantsan ne domin kaucewa haddasa fitina tsakanin kasashen biyu.

Asalin hoton, Frank Pellegrino
Daga karshe jakadan ya sanar da Pellegrino cewa jami'an Qatar sun yi ikirarin sun rasa inda Khalid yake "Mun ji takaicin wannan labari, fushi da takaici a kan jin wannan labari"
Amma ya yarda cewa a tsakiyar shekarun 90 ba a ganin Khalid a matsayin babban abin da aka sa a gaba ba. Pellegrino bai ma iya sanya shi cikin jerin Manyan 'yan ta'adda 10 na duniya ba, sai aka ce min an gaya min akwai 'yan ta'adda da yawa a a duniya."
Da alama an sanar Khalid aniyar Amurka ta kama shi.
A cikin 'yan shekaru bayan haka, sai sunan KSM ya ci gaba da bazuwa a duniya, yana bayyana wa a fili cewa yana da alaka da kungiyoyin ta'addanci na duniya, lokacin ne ya ziyarci Bin Laden sannan ya gabatar masa da wannan shiri na horar da matuka jiragen sama don su aiwatar da harin na 911.
Kwatsam kuma sai harin na 911 ya auku, bayan da wani da aka kama ya bayyana sunansa, ''Sai kuwa kowa ya fara cewa ahaf !, wannan mutumin Pellegrino ne ai'' inji shi. "Lokacin da muka gano cewa shine babu wanda ya fi ni bakin ciki."

Asalin hoton, Getty Images
A 2003, an bi sahun Khalid Sheikh Mohammed a Pakistan. Pellegrino ya yi fatan za a gurfanar da shi kan zargin da ake yi masa, Amma sai ya bace.
Da farko Hukumar leken asirin ta CIA ta kai shi wani "wurin bakar fata" inda aka yi amfani da "ingantattun dabarun yin tambayoyi".
"Ina so in san abin da ya sani, kuma ina son in sani cikin sauri," in ji wani babban jami'in CIA a lokacin.
An saka Mohammed cikin ruwa akalla sau 183, wani abu da aka kwatanta da "kusa da nutsewa". An shayar da shi ruwa ta dubura, matsin lamba iri iri, rashin bacci, tsiraicin tilas, kuma an ce za a kashe yaransa.
A lokacin ya bayar da bayanai da dama Amma rahoton Majalisar Dattawa daga baya ya gano cewa mafi yawan bayanan ya bayar na bode ne.

Asalin hoton, Getty Images
Bayan an bayyana cikakkun bayanai game da binciken na CIA, "sai aka mayar da manyan ɗaurarrun da aka kama kamar Khalid kurkukun Guantanamo a 2006. Daga karshe an ba FBI damar shiga.
A watan Janairun 2007 Frank Pellegrino ya hadu da mutumin da ya dade yana nema.
Mutanen sun zauna a tebur guda da juna.
"Ina so in sanar da shi cewa na fara bincikarsa tun shekarun 1990, sannan a nemi wasu bayanai ," in ji shi.
Tsohon jami'in na FBI ba zai bayyana yadda tattaunawarsu ta kasance daki daki da Khalid ba, ya bayyana hakan ga BBC cikin wasa da barkwanci.
Bayan kwana shida suna magana a karshe Khalid ya ce ya gaji haka nan a kyale shi," in ji Pellegrino.
Ƙoƙarin da aka yi na ba da gaskiya don 9/11 ya ɓace. Shirin gudanar da shari'a a New York ya baci bayan adawar jama'a da siyasa. "Kowa yana ta kururuwa 'Ba na son wannan mutumin a bayan gida na. Ku ajiye shi a Guantanamo,'" in ji Pellegrino, da kansa New Yorker.

Asalin hoton, Reuters
Lauyan da ke kare wanda ake zargi wato Nevin ya fara kare shi ne tun a 2008. kuma tsarin farko na shari'ar shi ne ana yi ba kakkautawa kafin daga baya aka zo ana jan kafa.
A yanzu haka an nada sabon alkalin da zai jagoranci shari'ar kuma shi ne na takwas da aka nada tun farkon fara ita wannan shari'a zuwa yanzu.
Sannan wabi abu ma shi ne dole ne alkalin ya karanta dukkan bayanan shari'ar, da yawansa ya kai kusan shafuka dubu talatin da biyar domin ya fahimci inda ma aka sanya gaba tukuna.

Asalin hoton, Pool
Nevin ya ce "Muna aiki tukuru don kada mu yi wani abu da zai kara tsananta wahalar Khalid da wadanda aka kama da suka sha tsawon shekaru,''
Wani dalili kuma da ya yi imanin kotun ta ja da baya shi ne saboda shari'ar kisa ce kuma hakan yana tayar da hankali. "Da tuni an gama idan gwamnati ba ta neman kashe wadannan mutanen."
Pellegrino ya jinkirta ritayarsa daga FBI da shekaru uku da fatan za a kammala shari'ar Mohammed, wanda yake sa ran zai bayar da shaida a kansa. "Zai yi kyau in ga wannan."
Amma tsohon jami'in na FBI ya yi ritaya, kuma ya bar hukumar.
Bayan ya shafe shekaru yana yawon neman Khalid, a yanzu Pllegrino na jin cewa ya gaza, yana ganin cewa da ace an kama shi tun 1990 da kuwa an kare aukuwar harin na 911.
"Sunansa na dawo min a kwakwalwata a kowace rana, kuma ba tunani ba ne mai daɗi," in ji shi.











