Amurka: Ambaliya ta hallaka sama da mutum 40

Asalin hoton, Others
Sama da mutane 40 ne zuwa yanzu aka tabbatar ambaliyar ruwa da ta afka wa yankin arewa maso gabashin Amurka ta hallaka tare da barnata gidaje.
Mamakon ruwan sama da guguwa mai karfin gaske da ke tafe da ruwa da aka yi wa lakabi da Ida ta haddasa ya addabi yankuna da yawa na New York da New Jersey da Connecticut da kuma Pennsylvania.
A birnin New York, kusan mutane 12 ne ruwa ya ci a gidajensu da ke karkashin kasa.
Shugaba Biden ya dora alhakin bala'in a kan sauyin yanayi kuma ya ce sai kasar ta shirya sosai domin fuskantar yanayi mai tsanani.

Asalin hoton, Reuters
Wannnan mummunar ambaliya da ta bayyana bakatatan ta shammaci kusan kowa da kowa a wannan yanki ba da tsammani ba ko alama, ballantana a ce an shirya mata.
Ruwan ambaliyar da guguwar mai karfin gaske da ke tafe da ruwa ya mamaye hanyoyin karkashin kasa, inda ruwa ke bankar jiragen kasa da ke bin wadannan hanyoyi na rami.
Tituna sun zama koguna, sannan kuma ambaliyar ta ratsa da mutane da dama a cikin gidaje ko dakunansu na karkashin kasa.
Wannan shi ne bala'i mafi tsanani da ba wani ya hadasa ba, wanda ya taba faruwa a yankin tun bayan mummunar guguwar nan mai ruwa ta Sandy da ta auku a 2012.
Shugabar garin Elizabeth a jihar New Jersey Chris Bollwage, inda nan ma aka samu irin wannan barnar ta ce wannan ita ce ambaliya mafi muni da suka taba gamuwa da ita a rayuwarsu ta shekara hamsin.
Ita ma Gwamnar Birnin New Yorkor, Kathy Hochul, wadda ta dare wannan kujera tsawon kasa da mako biyu ta ayyana dokar ta-baci.
Tana gargadin jama'a da cewa matsalar sauyin yanayi fa tana nufi ne da cewa, su daura damara ta kwana da sanin aukuwar irin wadannan bala'o'i a kai a kai.

Asalin hoton, MULLICA HILL LIVING
Shugaba Joe Biden ma cewa ya yi magance matsalar abu ne da ya zama na ko a mutu ko a yi rai, da ke bukatar daukar gagarumin mataki na zuba jari na sosai domin magance matsalar.
A ranar Juma'ar nan Shugaban zai ziyarci Louisiana ya duba irin barnar da guguwar mai ruwa ta Ida ta yi lokacin da ta fada a can ranar Lahadi. Sama da gidaje 900,000 ne ba su da wutar lantarki a jihar.
Magajin garin New York Bill de Blasio ya soki masana masu hasashen yanayi yana cewa hasashensu ya zama shirme cikin dan lokaci da yinsa.
Ya ce sun yi gargadin cewa a yi tsammanin samun ruwan sama da tsawonsa ya kai inchi uku zuwa shida a tsawon rana.
Amma kuma sai ga shi an yi ruwan da ya kai tsawon inchi 3.15 a Central Park a cikin sa'a daya kawai.
Ya ce saboda haka akwai bukatar a rika gaya wa mutane cewa abubuwa za su iya fin yadda ake tsammani a ko da yaushe.
Tuni duniya ta kara dumi da kusan maki 1.2 a ma'aunin selshiyas tun lokacin da aka fara samun habakar masana'antu, kuma dumin zai ci gaba da karuwa har sai gwamnatocin kasashen duniya sun dauki kwararan matakai na rage hayaki mai gurbata yanayi.










