Fenty Beauty: Yadda sana'ar kayan kwalliya ta mayar da Rihanna biloniya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Manish Pandey da Lindsay Brown
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilan Newsbeat
- Lokacin karatu: Minti 3
Lokacin da Rihanna ta saki waƙar..."Better Have My Money" a 2015, wani zai yi tunanin tana magana ne game da ribar da ta samu daga wakokinta da suka yi fice "We Found Love" ko "Diamonds."
Amma kuɗin shiga ne da ta samu daga kamfanita na kayan kwalliya Fenty Beauty wanda shi ne babban tsanin da ya ta zama biloniya a makon da ya gabata.
Rihanna, mai shekara 33, ta ƙaddamar da kamfanin kwalliya Fenty Beauty a 2017 tare da haɗin gwiwar kamfanin kayan ƙasaita LVMH (Moët Hennessy Louis Vuitton).
Sashen Newsbeat na BBC ya tattauna da masana kwalliya domin ganin sirrin nasarorin kamfanin Fenty na Rihanna.
'Bambanci ba shinge'
Rihanna ta ce manufar Fenty shi ne don ya yi daidai da buƙatun "ko wace mace" tare da fatarsu.
A dukkanin kayayyaki na nakan yi tunanin: akwai buƙatar sama da wani abu na musamman ga baƙar mace, kamar yadda ta shaida Refinery29 a 2017.
Wannan jajircewar ita ce ginshiƙi ga marubuciyar ado Jessi Morgan
"Rihanna ta mayar da hankali ga bambance-bambancen ba tare da shinge ba. Ta tabbatar da samar da buƙatu ga kowa," a cewar marubuciyar mai shekara 28.

Asalin hoton, Instagram/Jessica Morgan
Ba wai kawai samar da kayan shafe-shafen da suka dace da baƙar fata ba ne.
Rihanna ta samar da abubuwa da za su dace da buƙatun kowa, kamar yadda Chinazo Ufodiama mai shirin Unpretty a podcast ta bayyana.
Fenty ya kasance ɗaya daga cikin kamfanoni da ba su karkatar da hankali kan samar da kayayyakin kwalliya da suka shafi mata kawai.
"Babbar manufar rashin mayar da hankali kan wani ɓangare na jinsi ya yi tasiri," in ji ƴar jarida Amber Graffland
"An shafe tsohon tunani na kwalliya ga matakai na shekarun mata."

Nasarar Fenty Beauty

Asalin hoton, Getty Images
Arzikin Rihanna ya kai kudi dala biliyan $1.7, inda aka kiyasta kusan dala biliyan $1.4 na fitowa ne daga darajar kamfanin kayan kwalliya na Fenty Beauty.
Mujallar Forbes - da ta sanar da cewa Rihanna ta zama biloniya - ta ce ita ke da mallakin kashi 50 na kamfaninta na kayan kwalliya.
Fitacciyar mawakiyar ta ƙaddamar da Fenty Beauty a kantina 1,600 a ƙasashe 17 a 2017.
Rahotanni sun ce kamfanin ya samu ribar dala miliyan 100 a ranakun farko na kamfanin.
Ta fi samun kuɗi fiye da takwarorinta fitattu masu sana'ar kayan kwalliyar kamar kamfanin Kylie Cosmetics na Kylie Jenner da KKW Beauty na Kim Kardashian da kuma kamfanin Jessica Alba, a cewar Forbes.
Sauran kudin Rihanna kuma sun fito ne daga hannun jarinta na kamfanin Savage X Fenty da darajarsa ta kai dala miliyan 270 da kuma kudin da take samu a waƙoƙinta da kuma shirin fim.

Jessica, wadda ke zama a London, tana cikin waɗanda suka ƙaddamar da fenty a Birtaniya a kantin Harvey Nichols.
Ta ce da farko mutane sun yi tunanin kayan kamfanin na ƙasaita ne. Amma kuma sai ya kasance mafi rahusa wanda za a iya samu a shagunan kan titi.
Wannan ne shi ne babban ƙalubalen kasuwa ga Jessica.

Asalin hoton, Getty Images
Ba yaudara
Shafin Fenty ya ce kamfani ne da ba ya gwajin kayayyakinsa da dabbobi
Amber ta ce wannan "ya yi tasiri sosai" wajen nuna babban kayayyaki.
"Yanzu zamani ne da masu sayen kaya suna da ilimi da masaniya kan abin da suke so. Suna sayen zuba kuɗinsu ne kawai inda suka fi samun natsuwa," a cewarta.
Jessica ta ƙara da cewa wannan wata dabara ce ta kasuwa domin tsira daga ce-ce-ku-ce daga kafofin sada zumunta.

Asalin hoton, Nicole Haines
Amber ta yarda cewa tasirin Fenty' a kafofin sada zumunta ya sa ta haskaka.
"Fenty ne na farko da ya ja hankali kuma yake magana kai-tsaye da zamani a yadda suke so."
Tasirin Rihanna
Yana da wahala a iya kawar da ƙarfin tasirin Rihanna ga nasarorin kasuwancin Fenty.
Yayin da kuma magoya baya ke jiran sabuwar waƙa da ba su gani ba tun 2016, amma la'akari da shafinta na Instagram da ke da yawan mabiya miliyan 103 ya nuna yawan mabiyan Fenty maimakon waƙa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Instagram

"Ina ganin abin da mutane suka fi so shi ne alaƙarta da kamfaninta. Domin za ka iya gani ta fi yin magana game da kayanta na kwalliya," in ji Jessica.
Kuma duk da ta zama biloniya amma bai hana ta ci gaba da kasuwancinta ba














