Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ahmadu Fintiri: Gwamnan Adamawa ya ce ba ya sha'awar komawa APC
Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ya musanta rahotannin da ke cewa zai fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC sakamakon rikicin shugabanci a matakin kasa da jam'iyar ta fada ciki kwanakin da suka gabata.
A kwanakin baya ne dai aka yi ta yaɗa jita-jitar cewa gwamnan na da ra'ayin komawa jam'iyya mai mulki ta APC, kamar yadda gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya koma APC daga PDP.
Sai dai a hira da Fintiri ya yi da BBC, ya bayyana cewa: "Lokacin da take da ma'ana, ina da buƙata ma ban je ba ballantana yanzu da ta lalace, ai jam'iyyar APC ta zama lalatacciyar masar da ko almajiri ba ya buƙat.''
Gwamnan ya bayyana cewa zai ci gaba da bayar da gudunmawa wurin gina jam'iyyar PDP inda ya ce suna fatan jam'iyyar ta su ce za ta samar da shugaban ƙasa a shekarar 2023.
Fintiri ya kuma yi tsokaci game da rikice-rikicen cikin gida na jam'iyyar ta PDP inda ya ce ba masallaci ba ce ko coci da za a ce za a zauna lafiya kamar ruwa a cikin randa, a cewarsa ba abin mamaki ba ne a rinƙa samun rikice-rikice a babbar jam'iyya kamar PDP.
Ya ce ko da kotu ta dakatar da shugaban jam'iyyar PDP, ba a ɓata lokaci aka naɗa sabo ba, amma ita jam'iyyar APC da aka ce tana zawarcinsa, daga samanta har ƙasa ba ta da shugabanci, in ji shi.
Gwamna Fintiri ya ce abu ɗaya kawai suka rasa a halin yanzu a matsayinsu na jam'iyya, kuma shi ne shugaban ƙasa inda ya ce suna fatan Allah zai ba su shugabancin a 2023.
Sai dai ko da BBC ta tambaye shi alaƙarsa da tsohon mataimaki shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar, sai ya ce shugaba ne kuma uba ne a wurinsa.
Ya bayyana cewa ba abin mamaki bane idan ya karkata a wurin Atikun ba duk lokacin da lamura na siyasa suka taso domin jiharsu ɗaya kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne
Ko da aka tambaye shi batun zaɓinsa na wanda zai jagoranci Najeriya a 2023, sai ya ce "Allah ne zai yi zaɓi 2023, kuma muna roƙonsa muna sa tsammani, cikin kyautar da yake yi na mulki, ya ba wanda zai riƙe amanar wannan ƙasar.