Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yunkurin samar da ingantaccen makewayi a jihar Adamawa
Asusun Kula da Kara na Majalisar Dinkin Duniya Unifef ya ce yana fargabar Najeriya ba za ta iya cimma muradin kawo karshen yin ba-haya a waje ba daga nan zuwa 2025.
A bara, binciken Unife ya gano cewa 23% na mutanen Najeriya - kimanin mutum miliyan 47 – har yanzu suna yin ba-haya a waje a duk fadin Najeriya.
BBC ta duba lamarin a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya don ganin yadda wata hanya mai sauki ke taimakawa wajen shawo kan lamarin.