An sace dalibai da dama a wata makaranta a Maradun na jihar Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun ce 'yan bindiga sun kai hari wata makarantar maza da mata da ke karamar hukumar Maradun kuma sun sace dalibai da dama.

Mazauna garin Kayan Maradun sun shaida wa BBC Hausa cewa 'yan bindigar sun kai harin ne da safiyar Laraba kuma sun sace daliban da ya zuwa yanzu ba a kai ga sanin adadinsu ba.

Rahotanni sun ce dalibai fiye da 400 ne suke makarantar lokacin da aka kai harin suna masu karawa da cewa daliban suna rubuta jarrabawar 'Mock' ta 'yan aji biyar ne lokacin da aka kai harin.

Wani malamin makarantar ya shaida mana cewa lamari ya faru ne "muna shirye-shiryen yin jarrabawar mock ta 'yan aji biyar, bayan mun fito mun yi wa 'yan SS II bayani mun fito mun tunkaro dakin malamai, muna zaunawa sai kawai muka ji kukan babura sun tunkaro makaranta."

A cewarsa, daga nan ne suka watse suka shiga cikin gonar gero tare da wasu daliban amma duk da haka 'yan bindigar sun kwashe dalibai da dama.

Sai dai kawo yanzu hukumomi ba su tabbatar da adadin daliban da aka sace ba.

Amma malamin ya ce daliban da ke makarantar suna da yawa sosai lokacin da maharan suka shiga.

Wannan lamari na faruwa ne kwanaki kadan bayan gwamnatin jihar Zamfara ta dauki wasu sabbin matakai na kawo karshen hare-haren 'yan bindiga.

Matakan sun hada da hana bude kasuwannin da ke ci mako-mako da takaita yawan man fetur din da za a sayar da sauransu.

Me hukumar makarantar ta ce?

Wani malami a makarantar da ya bukaci kada a ambaci sunansa ya ce, an sace dalibai fiye da 70.

"Mun gano an sace yara 76 gaba daya, mata 53 sai maza 23. An sace malami daya, sannan an harbi yaro daya wanda yanzu yake asibiti ke karbar magani.

Mun kididdge yawan yaran ne bayan da iyaye suka zo muka dinga duba rijista muna gane wadanda ba sa nan.

Malamin ya ce dama babu jami'in tsaro ko daya a makarantar daga kan soja zuwa dan sanda da na civil defence, "ba makarantar ba kawai garin baki daya babu jami'an tsaro.

"A yanzu makaranta ta zama tarihi mun rufe mun tura kowa gida. Fatanmu dai Allah Ya fito da yaran nan don iyaye sun kadu matuka.

"Manyan jami'an tsaro sun zo an tattauna sun yi mana alkawarin cewa za su bi sawu," in ji shi.

Wata uwa

Wata uwa da ƴarta ke makarantar ta ce an kwaso wasu yaran da suka ɓuya a cikin daji a sume wasu ma ba rai aka tsinto su.

"Mu a yanzu ma ba mu san inda namu ƴaƴan suke ba tukun. Na tabbata yaranmu na cikin wadanda aka ɗauke don an ce da mota suka zo har gaban makarantar aka kwashe su.

"Masu wayon suka gudu su kuma kananan tsautsyi ya rutsa da su. Yarana biyu nake fargabar an dauke.

"'Ya'yan nawa shekararsu goma-goma suna aji daya na sakandare."

Ta yi kira ga gwamnati da a ceto 'ya'yansu a kuma kawo karshen wannan matsala.

"Idan aka ci gaba da yin haka to so ake a bar karatun a zauna a jahilce ko yaya?, in ji ta.

Me gwamnatin jihar ta ce?

Tuni dai gwamnatin jihar Zamfaran ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantu a fadin jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar wanda ya tabbatar da daukar matakin ga manema labarai, ya ce matakin ya shafi makarantun sakandare da na firamare.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara CP Ayuba Elkana a yayin da yake zanta wa da manema labarai a birnin Gusau, ya ce Gwamna Muhammad Bello Matawalle ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandiren ne a wani mataki na kyautata al'amuran tsaro a jihar.

Haka kuma CP Elkana ya ce gwamnan jihar ya bayar da umarnin sanya dokar hana fitar dare a dukkanin kananan hukumomin jihar 14.

Wannan matakin dai na zuwa ne bayan da wasu 'yan bindiga suka kai hari makarantar maza da mata da ke Kaya cikin karamar hukumar Maradun inda suka sace dalibai da dama.

Amma kwamishinan 'yan sandan bai yi wani karin haske game da yawan daliban da aka sace ba.

Matsalar garkuwa da mutane don neman kudin fansa na neman zama ruwan dare a Najeriya duk da ikirarin da hukumomi ke yi cewa suna daukar matakan takile al'amarin. Tun watan disambar bara fiye da dalibai dubu daya ne aka sace a kasar, sai dai an saco da dama daga cikinsu bayan da aka biya kudin fansa.