Rashin tsaro: Abin da ya sa wasu jihohin Najeriya suke rufe kasuwannin mako-mako

Wani dan bindiga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mahukunta sun ce an dauki matakin ne domin hana 'yan bindiga sakat
    • Marubuci, Imam Saleh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Wasu jihohi a arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da daukar matakan rufe kasuwannin da ke ci mako-mako a yankin da karin wasu matakai, a wani al'amari da masana ke ganin a matsayin fara samun hadin kai a tsakaninsu domin shawo kan hare-haren 'yan bindiga masu satar mutane.

Jihohin sun sanya doka kan sayar da man fetur, inda daga yanzu ba a yarda kowa ya sayar da man fetru a cikin unguwa ko a gefen titi ba.

Jihohin da suka dauki wannan mataki sun hadar da Katsina da Zamfara da kuma Kaduna, kuma dukkansu sun ce matakin na da nasaba da kokarin ganin sun toshewa 'yan bindigar duk wata kofa ta sararawa ko ta samun kayan da suke amfani da su wajen kaddamar da hare-hare.

Da ma masana tsaron sun jima suna cewa matsawar jihohin ba su hada kai ba, duk wani mataki da za su dauka ba zai yi wani tasiri ba.

Short presentational grey line

Me yasa ake daukar wannan mataki ?

Kasuwar kayan gwari

Asalin hoton, Getty Images

Masana tsaro na da ra'ayin cewa jihohin na daukar wannan mataki ne saboda sun gaji da yadda jama'a ke korafi a kan matsalar hare-haren 'yan bindiga da satar jama'a da a yanzu ta zama ruwan dare a yankunansu.

Tsofaffin sojojin da suka san harkar tsaro gaba da baya, sun shaida wa BBC cewa gwamnonin na ganin cewa daukar wannan mataki na iya zama silar kawo karshen matsalar da ake ganin ta gagare su, musamman yadda ake yawan ɗora alhakin halin da jihohinsu suke a kansu, maimakon dora alhaki a kan gwamnatin tarayya, wadda ita ce take da iko a kan jami'an tsaro.

A wata hira da BBC Hausa, Kwamishinan Tsaro na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce daga abubuwan da ake ganin suna faruwa a halin da ake ciki, za a fahimci cewa an samu hadin kan da ake bukata tsakanin jihohin da suka fi fama da matsalar tsaro, musamman ta fuskar yin aiki tare domin shawo kan rashin tsaron da ke addabar jihohin.

Shi kansa wannan kalami da ya fito daga bakin Kwamishinan Tsaron na jihar Kaduna, masana tsaron na ganin cewa da alama jihohin da suka fi fama da matsalar sun fara amsa kiran da ake yi musu na su hada kai domin yaki da matsalar.

Short presentational grey line

'An yi ba a yi ba'

'Yan sandan Najeriya

Asalin hoton, AFP

Sai dai yayin da gwamnonin wadannan jihohi ke ganin sun dauki matakin da ka iya taka rawa wajen magance wannan matsala, wasu daga cikin masana harkar tsaro a Najeriya na ganin cewa wannan mataki ba zai yi wani tasiri ba.

Manjo Yahaya Ibrahim Shinku mai ritaya, tsohon jami'in sojin Najeriya ne, ya shaida wa BBC Hausa cewa idan gwamnonin na ganin cewa sun toshewa wa yan bindigar kofar sararawa ne, to akwai sauran rina a kaba.

"Da ma fa mutanen nan sun saba satar mutane daga wani garin su yanka ta daji su dangana ta wani garin, don hakan idan ka ce ka hana sayar da man fetur a inda suke kana ganin ba za su je wani wajen su sayo ba ?" , in ji masanin.

Ya kara da cewa "Hakan na iya za sa 'yan bindigar su ce to bari su fara neman mutanen da suka sacewa 'yan uwa su kai musu abinci da man fetur tun da su an toshe musu kofa."

A cewar Manjo Yahaya Ibrahim Shinku, karshe dai wannan mataki zai kare ne a kan su jama'ar gari talakawa wadanda suka dogara da kasuwannin da ke ci a kowanne mako, da kuma wadanda ke dogara da harkar bunburutu, wato sayar da fetur a cikin unguwa.

Short presentational grey line

Hakan na da tasiri

Sojojin Najeriya

Asalin hoton, NDHQ

Ko da yake shi ma Manjo Sadiq Galma mai ritaya ya amincewa cewa wannan mataki da gwamnonin jihohin suka dauka zai shafi rayuwar talaka, ya ce hakan kuma zai taka rawa wajen ganin an hana 'yan bindigar sakat.

A cewarsa "Da ma an jima ana mamakin ta inda mutanen ne ke samun man fetur tunda ana ganinsu a kan babura, don haka daukar wannan mataki ba shakka zai taimaka, sai dai maganar rufe kasuwanni ba zai kawo wani sauyi ba.

Ya ce: "Wasu mutane na cika tankunansu suna kai wa wadannan mutane a daji, wasu ma suna kai musu fetur a motocin itace a saya da yawa a gari a kai musu, to tunda har gidajen mai ma an hana su bayar da mai a jarka a yankunan da matsalar take, ba shakka zai haifar da sauyi."

Ya kara da cewa shi kansa wannan mataki da gwamnonin suka ɗauka gwaji ne, don haka idan sun lura bai yi wani tasiri ba za su bullo da wata hanyar ta daban.

Sai dai a matsayinsa na masanin tsaro, ya ce ''"Matakin zai yi tasiri ta wata hanya, amma daga karshe bazai yi wani tasiri da ake tsammani ba," in ji Manjo Galma mai ritaya.