Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
William Ruto: Yadda mutumin da ke 'turin' baro kuma ya taɓa tallan kaji yake son zama shugaban Kenya
- Marubuci, Daga Emmanuel Onyango
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Nairobi
Mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto ya bulo da salon neman amincewar masu kada kuri'a a zaben da za a yi a kasar a shekara mai zuwa inda yake amfani da salon tura wul baro da kuma jaddada cewa ya taba tallan kaji, duk dai domin ya nuna cewa takarar zaben ta rabu ne tsakanin "masu fafutukar neman na kansu" da kuma " 'yan na-gada".
A kasar Kenya, kamar yadda sunan ya nuna, masu fafutukar neman na kansu na nufin - musamman matasa - wadanda suke fafutukar neman kudi a yanayin tattalin arzikin da ke da wahalar sha'ani.
A gefe guda, 'yan na-gada na nufin mutanen da suka fito daga attajiran iyaye wadanda suka mamaye harkokin siyasa - da kuma tattalin arziki- tun da kasar ta samu 'yancin kai daga Birtaniya a shekarun 1960.
An sanya Shugaba Uhuru Kenyatta da dan siyasar hamayya Raila Odinga a rukunin 'yan na-gaba.
Uhuru Kenyatta ɗa ne ga shugaban Kenya na farko, yayin da shi kuma Raila Odinga, ɗa ne ga mataimakin shugaban kasar na farko, ko da yake Mr Odinga ne ɗan siyasar Kenya da ya fi daɗewa a kurkuku saboda siyasa kuma shi ne ya jagoranci fafutikar kawo sauyi a harkokin siyasar kasar.
Mr Ruto, mai shekara 54, shi ne ya kirkiri kalmar "masu fafutukar neman na kansu" a matsayinsa na dan siyasa na cike da kazar-kazar da buri mai girma.
Ya bayyana yadda ya rika zuwa makaranta ba tare da talakmi ba, da kuma yadda ya sayi takalminsa na farko yana da shekaru 15, da ma yadda ya "rika sayar da kaji a gefen titi".
Sakin auren siyasa
A kwanakin nan Mr Ruto yana raba wul baro, da tankokin ruwa ga marasa aikin yi, lamarin da ya sa matasa suke kaunarsa.
Ya kulla kawancen siyasa da Mr Kenyatta a lokacin zabukan 2013 da 2017, abin da ya sa suka yi nasara.
Wasu sun kalli kawancen a matsayin wanda ba zai dore ba saboda mabambantan tarihinsu.
Tuni dai 'yan siyasar biyu suka raba gari, amma Mr Ruto yana ci gaba da zama a matsayin mataimakin shugaban kasa, saboda kundin tsarin mulkin kasar da ya tabbatar da 'yancin mataimakin shugaban kasa.
Yana fatan zama shugaban kasa a shekara mai zuwa, a zaben da zai fafata da Mr Odinga, mai shekara 76 wanda - a wani mataki na juyin waina a siyasar Kenya - shi ne yanzu yake ɗasawa da Mr Kenyatta.
Mutanen biyu sun yi raddi kan yakin neman zaben Mr Ruto inda suka bullo da shirin da aka yi wa lakabi da "hadin gwiwa tsakanin masu bambancin ra'ayi", wanda suka ce zai inganta sha'anin tafiyar da mulki.
Hakan ya hada da kirkikar ofishin firaministan. Lamarin ya sanya ana jita-jita cewa Mr Kenyatta ne zai rike wannan matsayi a cikin gwamnatin da Odinga zai jagoranta.
Sai dai a wani mataki na yin cikas ga mutanen biyu, a makon jiya Kotun Dakaka Kara ta amince da hukuncin wata Babbar Kotu da ya ayyana matakin a matayin wanda bai halatta ba, tana mai cewa majalisa ce kadai - ba shugaban kasa ba - za ta iya gyara kundin tsarin mulkin kasar. Gwamnati ta nuna cewa za ta daukaka kara zuwa Kotun Koli.
'Babbar rashin jituwa'
Mr Ruto - wanda ya nemi goyon baya a zabukan da suka gabata a wani shiri da ya yi wa taken "Kasar masu fafutika" - yanzu yana amfani da salon inganta tattalin arziki ta hanyar tsarin "kasa zuwa sama", yana mai cewa hakan zai amfani talakawa, musamman matasa, wadanda suke shan matsin tattalin arziki sakamakon annobar korona.
Alkaluman rashin aikin yi tsakanin 'yan shekara 18 zuwa 34 ya kusa kashi 40, kuma tattalin arzikin kasar ba ya samar da isassun ayyukan yi ga matasa 800,000 da ke shiga jerin marasa aikin yi duk shekara.
Masu hamayya sun yi watsi da shirin Mr Ruto na tsarin bunkasa tattalin ariki "daga kasa zuwa sama" suna mai bayyana shi da cewa shifcin-gizo ne kawai.
"Da alama wannan shiri ne kawai na bai wa talakawa kudi. Bai yi kama da shirin bunkasa tattalin arziki ba," a cewar masanin tarihi Ngala Chome.
Mr Odinga, wanda sau hudu yana shan kaye a yunkurin zama shugaban kasa, ya bayyana shirin Mr Ruto a matsayin "shirme", yana mai cewa ba za a inganta tattalin arziki ba ba tare da tabbatar da daidaito a harkar siyasa da shugabanci ba.
Babu tantama cewa tsarin Mr Ruto na gina "Kasar masu fafutika" ya janyo ce-ce-ku-ce game da hakikanin tsarin siyasar Kenya tun daga samun 'yancin kanta.
"Mutanen da suka karbi mulki tun bayan mulkin turawa har yanzu su ne suke iko da kasar nan. Wannan babban abu ne da ya kamata a duba idan ana son fahimtar tsarin siyasar Kenya," a cewar Mr Chome.
Mr Ruto ya bayar da fifiko kan karfafa dangantaka tsakaninsa da matasa da talakawa. 'Yan takarar da ya goya wa baya sun lashe zaben cike-gurbi na kujeru uku na majalisar dokokin
Ya zuwa yanzu ba ya sanya kabilanci a yakin neman zaben da yake gudanarwa - wani abu da ya kasance kanwa uwar gami game da siyasar kasar wanda a baya ya haddasa rikicie-rikicen bayan zabe.
"An samu sauyi a siyasar Kenya. Yanzu mutane suna tattaunawa a kan tattalin arziki a wuraren yakin neman zabe ba kamar yadda yake a baya ba," in ji Mr Chome.
Baa san asalin kudinsa ba
Kazalika akwai wasu tambayoyi da ake yi game da ikirarin Mr Ruto cewa yana son kawo sauyi.
Ana zarginsa da cin hanci a gwamnati sannan kuma ana tababa kan yadda ya samu kudinsa.
A watan Yunin 2013, wata Babbar Kotu ta umarce shi ya bayar da gonarsa mai fadin kadada 100 sannan ya biya wani manomi da ya zarge shi da kwace masa gona bayan rikicin zaben 2007.
Ya dage cewa ba shi da laifi a yana mai karawa da cewa ya samu kudinsa ne ta hanyar yin aiki tukuru.
Batun kudi yana da muhimmanci a siyasar Kenya saboda ba a yi komai sai da kudi - 'yan takara suna kashe dubun dubatar daloli ba tare da tabbacin yin nasara ba.