Rikicin Afghanistan: 'Shin duniya ta damu da abin da ke faruwa a nan?'

Asalin hoton, EPA
Mako guda bayan da Taliban ta kwace mulkin Afghanistan, 'yan kasar da dama na cike da rashin tabbas kan yadda tsaron lafiyarsu da rayuwarsu za su kasance.
A nan, wata daliba matashiya ce take bayyana fargaba game da makomarta. BBC ba ta bayyana sunanta ba saboda dalilai na tsaron lafiyarta.
"Yau kwana na bakwai kenan tun bayan da kasar ta rushe, shugaban kasa ya tsere, kana Taliban suka sake karbe mulki.
An bar mu a baya ...
Fargaba na ci gaba da shiga daukacin zuciyata, kuma a duk kwanan duniya, nakan rika jin duk wani fata da nake da shi yana gushewa. Tsananin bakin ciki da damuwa sun maye gurbin farin ciki a zuciyata. Babu abin da nake iya gani sai duhu, rashin tabbas da rashin makoma mai kyau.
Tabbas za a kashe ni. Akwai dalilan da za su sanya a yi hakan...
Wannan shi ne yadda akan ji a lokacin da wadanda kake tsoro suka mamaye kasar.
Ka yi tunanin tafiya a kan wata doguwar hanya, wacce ba ta da karshe, da kuma yanayin hazo; kuma kai kadai.
Na fuskanci matsaloli da dama a rayuwata, da babu wata budurwa da za ta iya jurewa. Na kuma iya jure su, amma wannan...
Ke duniya, shin kin damu da abubuwan da ke faruwa a nan? Kin damu da mu kuwa? Kina ganinmu kuwa? Tambaya nake?
Ga wadanda suke sauraro, ga wadanda suka damu da mu, ina rubuta wannan. Ina fadin wannan.
Muna shan wahala a nan. An bar mu a baya. Zama cikin irin wannan fargaba ya fi mutuwa tsanani. Shi ne mafi muni.
Idan kuna sauraronmu, ku taimaka mana. Ku taimaka mana mu tsira, mu sake amincewa cewa akwai haske a gaba; mafi girma fiye da a baya.
Muna son kasarmu ta dawo. Muna so mutanenmu su yi rayuwa irin wacce suke so, irin wacce ta kamata.
Ku fada wa kasashenku su dakatar da yakin - yaki mummunan abu ne, yana da mummunar fuska, ba shi da gwani. Zuciya ta yi kankantar da ba za ta iya jure wa yaki ba, da kuma jure wa sakamakon abubuwan da yake haifarwa.
Mun zama ragowar yaki, wasu 'yan mata sun shiga cikin tsananin rashin tabbas, cikin fargaba, cikin wasu-wasi… neman wani wanda zai taimaka mana mu rayu.
Muna kallon iyalanmu tare da yin kuka saboda gaza yin wani abu.
Kallon sararin samaniya tare da tambayarsa: kana ganinmu, za ka taimaka mana? Ina yin fata, wannan kankanin fatan!
Ke duniya, ku mutane a wasu kasashe, kun yi sa'a! Ina mai sha'awar irin yadda kuke rayuwa.
Ku kalle mu. Ni ce mai cike da buri masu yawa, burin taimaka wa saura, amma yanzu ga shi ni nake neman taimako.
Wannan yaki. Shin zan taba cewa: Za mu kai labari? Zan iya?''











