'Yan bindiga sun sace 'yan Islamiyya takwas a Katsina

bandits

Rundunar jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ƴan bindiga sun sace yara ƴan makarantar Islamiyya takwas a garin Sakkai da ke ƙaramar hukumar Faskari.

Mai magana da yawun rundunar SP Gambo Isah ya tabbatar wa da BBC lamarin, wanda ya ce ya faru ne ranar Talata da yamma.

"Shekaranjiya da daddare muka samu labarin ɓarayi sun kai hari sun tare hanyar Sheme zuwa 'Yan Kara, jami'anmu sun kai ɗauki. Ashe daga baya sun shiga wani gari Sakkai.

"Sun shiga da niyyar ta'addanci, to a daidai lokacin yara yan Islamiyya sun taso daga makaranta, sai suka yi a tara a tara suka bi yaran suka kama su," in ji shi.

Amma SP Isah ya ce sai yaran suka tsere. "Sai dai labarin da muka samu daga mai unguwar wannan gari ya ce ba a ga yara takwas ba, wanda hakan ke nuni da cewa ƴan bindigar sun tafi da su."

SP Isah ya ce tuni rundunar ƴan sandan jihar ta ƙaddamar da bincike tare da bai wa jami'an tsaro umarnin bincikar dazuzzukan da suke wannan yanki don ceto yaran.

Wannan layi ne
Wannan layi ne

BBC ta tambayi mai magana da rundunar yan sanda ko jami'ansu ba su samu shiga garin Sakkai din ba bayan da suka je hanyar Sheme don kai ɗauki bayan samun rahoton.

Sai ya ce "da yake hankali ya karkata a kan abin da ya faru kan hanyar Sheme zuwa Ƴan Karan, ba mu samu rahoton abin da ya faru a Sakkai ba sai jiya (Laraba), domin ba a yi mana rahoto ba sai da muka tuntuɓi mai garin ƙauyen.

"Da muka tambaye shi dalilin ƙin yin rahoto sai ya ce ya shaida wa jami'an soji da aka girke kusa da garinsu can ya kai rahoton.

Kwanton ɓauna

Baya ga sace ɗaliban Islamiyyar ƴan bindigar sun kuma yi wa haɗakar jami'an tsaro kwanton ɓauna a hanyar Sheme zuwa Ƴan Kara har suka ƙona motoci uku, ɗaya ta jami'an tsaro, biyu kuma na matafiya.

Amma ya ce babu tabbas ko maharan sun sace wasu matafiya, kazalika SP Isah bai faɗa wa BBC ko ƴan bindigar sun kashe jami'an da suka yi wa kwanton ɓaunar ba.

Ya ce: "Muna kan bincike don tabbatar da ainihin abin da ya faru. Harkar tsaro harka ce da ba komai za ka yi bayani a gidan rediyo ba. Akwai wasu abubuwan da za mu bar su a hannunmu don gudun firgita al'ummar ko faɗar abin da bai kamata ba," in ji SP Isah.

Ƙaruwar sace ɗalibai

Jihar Katsina na daga cikin jihohin da hare-haren ƴan bindiga ya yi ƙamari a Najeriya.

Haka kuma wannan satar yaran ita ce ta baya-bayan nan cikin jerin sace-sacen ɗalibai da ke neman zama ruwan dare a Najeriya.

Masu sharhi na ganin hakan babbar barazana ce ga ilimi na zamani da na addini, musamman a yankin da dama ake kukan rashin ingantaccen ilimi tsakanin al'ummarsa.

Kuma sace ɗaliban na jefa rayuwar yara cikin gararamba da barin iyayensu cikin ɗimuwa.

Idan ba a manta ba har yanzu ɗaliban makarantar Islamiyyar Tegina fiye da 100 a jihar Neja na hannun ƴan bindigar, kuma mafi yawansu yara ne ƴan ƙasa da shekara shida.

Wannan lamari na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya umarci al'ummar jihar da ke fama da matsalar tsaro da su nemi makamai domin kare kansu.

Ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan harkokin watsa labarai, Abdu Labaran Malumfashi, ya fitar inda gwamnan ya ce tsaro ba aikin gwamnati ba ne kawai - dole ne jama'a su yi hoɓɓasa.

Gwamna Aminu Bello Masari ya yi wadannan kalaman ne yayin jajanta wa al'ummar da suka rasa 'yan uwansu a garin Jibia sakamakon take su da wata motar jami'an hana fasa kauri ta yi.

Sai dai masana harkar tsaro na ganin hakan gazawa ce daga ɓangaren gwamnati.

Wannan layi ne