An bayyana TikTok a matsayin manhajar da aka fi saukewa a 2020

Asalin hoton, Reuters
TikTok ce manhajar da aka fi saukewa a 2020 a yayin da ta kwace kambun da Facebook Messenger yake rike da ita, a cewar kamfanin bin diddigin alkaluman shafukan intanet Annie.
Manhajar ta kasar China ita ce kadai manhaja da ba mallakin Facebook ba da ta kasance cikin manyan manhajoji biyar da aka fi saukewa a duniya.
A kasar ta China, kamfanin ByteDance da ya mallaki TikTok shi aka fi amfani da shi tare da wata manhajar bidiyo da ke amfani da harshen China Douyin.
Manhajar ta TikTok ta samu karbuwa duk da yunkurin da tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi haramta ta.
Tun shekarar 2018 lokacin da aka soma bin diddigi kan shafukan intanet, manhajoji mallakin Facebook suke kan gaba a jerin wadanda aka fi saukewa kuma har yanzu su ne aka fi mu'amala da su.
Manhajojin kamfanin sada zumunta na Mark Zuckerberg su ne suka kasance sauran manhajoji hudu da suke a jerin wadanda aka fi saukewa - wato Facebook, WhatsApp, Instagram da Facebook Messenger.
A shekarar da ta gabata, tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan dokar haramta sauke manhajar TikTok a Amurka.
Gwamnatin Trump ta yi zargin cewa TikTok yana bazarana ga tsaron kasar saboda China tana karbar bayanai daga wurinsa. Sai dai kamfanin ya sha musanta zargin.

Asalin hoton, Getty Images
Tun da ya zama shgaban kasa a watan Janairun wannan shekarar Joe Biden ya soke dokokin da Mr Trump ya kafa.
A makon jiya, an bayyana cewa TikTok yana gwada wani tsari da zai sa bayanan da aka wallafa a cikinsa su rika bacewa kamar yadda yake faruwa a Snapchat, Facebook da Instagram.
TikTok zai bar masu amfani da manhajar damar ganin abubuwan da mutanen da suke bi suka wallafa a shafukansu tsawon sa'a ashirin da hudu kafin su goge.












