Gwamnati ba ta kyauta mana ba - Iyayen ɗaliban da aka sace

Wasu iyayen ɗaliban da ƴan bindiga suka sace daga makarantunsu a Najeriya sun shaidawa BBC cewa ba su ji dadin kalaman ministan ilimi ba, da ke cewa gwamnati ba za ta sasanta da masu garkuwa ba.
A ranar Laraba bayan taron majalisar zartarwa a Abuja, ministan Chief Chukwuemeka Nwajiuba ya shaida cewa ɗaya daga cikin dalilan gwamnati na dakatar da sasanta da ƴan bindiga shi ne kamar ana basu damar sake gina kansu ne, da ci gaba da haifar da barazana ga tsaron ƙasar.
Sai dai ministan ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da bin sauran hanyoyin da suka dace domin ganin ta kuɓutar da ɗaliban.
Ɗaya daga cikin iyayen yaran, Abdulkarim Kontagora wanda aka ɗauke yayansa uku daga makarantar sakandaren tarayya ta Yauri, ya ce shawarar mahukunta ba daidai ba ne musamman a wannan lokaci da ya kamata gwamnati ta jadada musu kokarin dawo da yaransu gida.
"Abin da gwamnati ta ce ya yi mun ciwo matuka kuma na ji baƙin ciki saboda wannan lokaci ne da muke bukatar taimakonsu domin yaranmu su dawo gida, kuma yanzu su fito suna cewa ba za su tattauna da ƴan bindiga ba ai tamkar suna nufin kowa na shi ya fishe shi kenan.
Mahaifin da ɗaya daga cikin ƴaƴansa ya kuɓuta daga hannun ƴan bindiga ya shaida ce maharan sun shaida cewa su da gwamnatin tarayya za su tattauna ba gwamnatin Kebbi da makarantar take ba.

"Shugaban ƴan bindiga ya shaida mana cewa shi da gwamnatin tarayya zai tattauna ba gwamnatin Kebbi ba, kuma wannan kalamai ba abin farin ciki ba ne a gare mu."
Mercy Audu da ke da yara uku da aka sace daga makarantar Bethel High School na Kaduna ta ce shawarar da gwamnati ta yanke na jadada musu cewa Ubangiji ne kawai zai musu mafita.
"Ubangiji ne kawai zai taimakemu a wannan yaƙi saboda tun farkon wannan matsala bamu ga alamun gwamnati dagaske take yi ba wajen taimaka mana."
A wannan lokaci daruruwan daliban Najeriya na hannun masu garkuwa da su a yankuna daban-daban na ƙasar, kuma akasari iyayye ke hada kudin fansa wajen ceto yaransu.
Ga wasu daga cikin manyan garkuwa da aka yi kan ɗalibai a Najeriya
Ɗaliban makarantar Kankara
A ranar 11 ga watan Disamban 2020 ƴan bindga suka shiga makarantar kimiya ta sakandaren Kankara da ke Katsina tare da awon gaba da ɗalibai sama da 300.
Ɗaliban Kagara
A ranar 27 ga watan Fabarairu ƴan bindiga suka shiga makarantar sakandare a jihar Neja tare da garkuwa da ɗalibai kunsa 50.
Makarantar Jangebe
A ranar 2 ga watan Maris ƴan bindiga suka kai hari makarantar mata ta garin Jangebe da ke jihar Zamfara kuma sun sace daruruwan ɗalibai mata.
Jami'ar Greenfield
A watan Maris din 2021 ƴan bindiga cikin tsakiyar dare sun kai hari jami'ar Greenfield da ke Kaduna tare da garkuwa da ɗalibai 30.
Kwalajen forestry
A ranar 15 ga watan Maris ƴan bindiga sun kai hari wannan kwalajen da ke kusa da makarantar sojoji ta NDA a Kaduna tare da kwashe ɗalibai kusan 100.
Kwalajen Tarayya na Yauri
A ranar 16 ga watan Yuni 2021, gungun ƴan bindiga suka kai hari a makarantar da ke jihar Kebbi a arewacin Najeriya da kwashe sama da ɗalibai 100 cikin daji.












