Jelani Aliyu ya bude tashar cajin mota mai amfani da hasken rana a Lagos

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Shugaban hukumar zayyana motoci da tsara su ta Najeriya wato NADDC, Jelani Aliyu, ya kaddamar da tashar cajin mota wacce take amfani da hasken rana.

An bude tashar ne a birnin Lagos da ke kudu maso yammacin kasar ranar Talata.

An kaddamar da tashar ne da zummar rage amfani da fetur, wanda bisa al'ada yake gurbata muhalli.

Wasu bidiyon da za ku so ku kalla