Jamhuriyar Nijar: Kalaman Mohamed Bazoum sun jawo cacar baki tsakaninsa da sojojin Mali

Al'ummomin Jamhuriyar Nijar da na Mali na ci gaba da cacar baki kan shaguɓen da shugaban Nijar ɗin ya yi game da sojojin da ke mulkin ƙasar ta Mali.

Shugaba Mohamed Bazoum ya soki sojojin da ke mulkin Mali yayin da yake halartar taron ƙasashen ƙungiyar G5 Sahel a Faransa ranar Juma'a, 9 ga watan Yuli.

"Ya zama dole mu hana sojoji hawa mulki saboda suna da rauni a fagen daga wurin da ya kamata su kasance," in ji Bazoum yayin da yake magana game da ƙasar Mali.

Kalaman nasa sun jawo zazzafar mahawara a shafukan sada zumunta tsakanin al'umomin ƙasashen biyu, a cewar wakiliyar BBC a birnin Yamai Tchima Ila Yusufu.

A martaninta, gwamnatin soja ta Mali ta gayyaci jakadan Nijar a Mali, Mamoudou Moumouni, domin bayyana masa damuwarta.

Sai dai yayin wata hira da kafar yada labarai ta gwamnati Shugaba Mohamed Bazoum ya nuna takaicinsa kan yadda 'yan Mali suka ɗauki waɗannan kalamai nasa.

Me Mohamed Bazoum ya ce?

Shugaba Mohamed Bazoum ya je birnin Paris na Faransa ne domin tattaunawa da Shugaba Emmanuel Macron game da ayyukan tsaro a yankin Sahel, wanda masu iƙirarin jihadi suka addaba.

Kazalika, ya halarci taron ƙungiyar ƙasashen na G5 Sahel ta intanet tare da sauran shugabannin ƙasashen duk da cewa shi kaɗai ne shugaban da ya yi tattaki zuwa Faransa domin taron.

Da yake jawabi a taron Bazoum ya taɓo alaƙa tsakanin mulki da kuma yaƙi da masu iƙirarin jihadi, inda ya nuna cewa aikin sojoji shi ne bayar da tsaro ba mulki ba.

"Wajibi ne mu hana sojoji zama shugabannin ƙasa ko ministoci. Wane ne zai yi musu yaƙi? Abu ne mai sauƙi a ƙasashenmu duk loƙacin da sojoji suka gaza kawai su zo su ƙwace mulki.

"Abin da ya faru kenan a Mali: A 2012, sojoji sun gaza amma sai suka yi juyin mulki. A shekarar ma a 2020, sun sake aikata hakan. Wannan abin Allah-wadai ne".

Wane martani Mali ta mayar?

Gwamnatin Mali da sojoji ke jagoranta ba ta bari lamarin ya kwana ba, inda Ministan Harkokin Waje Abdoulaye Diop ya gayyaci jakadan Nijar Mamoudou Moumouni a ranar Juma'ar domin bayyana masa matsayinsu.

A cikin wata sanarwa da ma'aikatarsa ta fitar, ministan ya fara da bayyana "mamakinsa" kan kalaman sannan ya nuna rashin jin daɗinsa a madadin gwamnatin Mali.

"Gwamnatin Mali na iya tunawa cewa ƙasar da Nijar waɗanda ke da alaƙa ta tarihi da kuma yanki, sun daɗe suna ƙawance wanda ya kamata a ƙarfafa shi. Sai dai waɗannan kalamai sun saɓa wa wannan ƙawancen.

"Tabbas ƙasashenmu na fama da matsaloli; yaƙi da tsattsauran ra'ayi da ta'addanci, ga kuma rikicin kiwon lafiya da annobar korona ta haifar, ya kamata a ce sun haɗa kan al'ummominsu wajen cimma buƙatunsu."

Ina magana ne da sunan 'yan uwantaka da maƙotaka - Bazoum

Bayan da ce-ce-ku-cen ya karaɗe ƙasashen biyu, Mohamed Bazoum ya mayar da martani, yana mai cewa "'yan uwantaka da maƙoataka" suka sa ya yi kalaman.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, shugaban ya ce "abu ne da ya shafi ƙasa da ƙasa kuma ina magana ne da sunan 'yan uwantaka.

"Ina so Mali ta fita daga halin da take ciki don haka a shirye nake na taimaka mata. Na yi hakan a lokacin da nake ministan harkokin waje har ma sai da wasu 'yan ƙasar suka ni ne ministansu na harkokin waje.

"Ni ne dai ban sauya ba game da Mali kuma ba zan taɓa sauyawa ba. Na kare Mali kuma zan ci gaba da kare ta ta kowace hanya."